Sport
Dollar
38,7516
0.36 %Euro
43,7236
0.39 %Gram Gold
4.160,1600
1.37 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ganawar ta sa an rattaba hannu kan yarjejeniyoyi ta fannoni daban-daban tsakanin ƙasashen biyu.
Ministan tsaron cikin gida na ƙasar Nijar, Birgediya Janar Mohamed Toumba, ya gana da shugaban jami’an tsaron ƙasar Iran, Birgediya Janar Ahmed Rezaei Radan game da matsalar tsaron ƙasar.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Nijar (ANP) ya ruwaito cewa an yi ganawar ne a birnin Yamai inda Birgediya Janar Ahmed Rezaei Radan ya jagoranci wata tawagar ƙasar.
Manyan jami’an ƙasashen biyu sun tattauna game matsalolin tsaro na cikin gida da suke fama da su, lamarin da zai sa su ayyana ɓangarorin haɗa kai, in ji ANP.
“Domin cim ma wannan, tattaunanwar ta mayar da hankali ne kan horarwa da musayar bayanai da kuma ƙwarewa wajen yaƙar laifuka da ta’addanci da kiyaye kan iyaka da kuma yaƙar fataucin miyagun ƙwayoyi,” a cewar rahoton.
Ƙasashen biyu sun amince da kafa wani kwamiti da zai ƙunshi ƙwararru daga ɓangarorin biyu wanda zai rika ganawa a ko wace shekara.
Wannan kwamitin zai rika ba da gudunmawa wajen musayar bayanai game da ‘yan ƙasashen biyu tare da jagorantar ko wane aiki da ke iya tasowa a shirin hukumar ‘yan sanda ta duniya da kuma yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa.
Kazalika ganawar ta yanke shawarar tura wasu ‘yan sanda da wasu jami’an tsaron Nijar zuwa jami’ar ‘yan sanda ta Iran, inda za a horas da su.
Ɓangarorin biyu sun yi bita game ayyuka a bakin daga da buƙatu na horaswa da tsare-tsaren musayar bayanai. Kuma an ba da bayanai game da tsarin dakarun tsaron Iran.
A ɓangaren Nijar, bayanin ya mayar da hankali ne kan ƙalubale irin na tsaro da kuma yanayin zamantakewa da siyasa tun ranar 26 ga watan Yuli na shekarar 2023 tare da batun ƙungiyar AES.
Ganawar ta sa an sanya hannu kan yarjejeniya ta fannoni daban-daban tsakanin ƙasashen biyu.
Daga bisani wakilan ɓangarorin biyu sun yi musayar kyaututtuka.
Comments
No comments Yet
Comment