Dollar

38,7786

0.39 %

Euro

43,8944

0.27 %

Gram Gold

4.147,5900

1.06 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Tattaunawar ta mayar da hankali kan haɓaka alaƙa a ɓangarori irin su zuba jari, kasuwanci, sufuri da makamashi.

Turkiyya, Amurka na son kyautata alaƙar tattalin arziki da dabarun haɗin kai

Ministan Kudi da Baitulmali na Turkiyya Mehmet Simsek ya gana da Sakataren Baitulmali na Amurka Scott Besent a Washington a ranar Laraba don tattauna fadada hadin kan tattalin arziki da dabarun ayyuka tare a yankunansu, in ji Ma’aikatar Kudi ta Turkiyya.


Gwamnan Babban Bankin Turkiyya Fatirh Karahan ma ya halarci ganawar inda ya halarci zmaan da masana suka kira “Yanayin Kawo Cigaba”.

Dukkan bangarorin biyu sun sake tabbatar da aniyar Shugaba Recep Tayyip Erdogan da Shugaba Donald Trump ta habaka alakar kasashen biyu kawaye a NATO.

Mayar da hankali ga kasuwanci, zuba jari da makamashi

Tattaunawar ta mayar da hankali kan haɓaka alaƙa a ɓangarori irin su zuba jari, kasuwanci, sufuri da makamashi. Simsek ya bayyana muhimmancin janye wasu ‘yan takunkumai da ke hana tafiyar da hadin kai a bangaren tsaro - bangare mai muhimmanci a alakar kasashen.

Tawagar Turkiyya ta kuma gabatar da cigaban daidaituwar tattalin arziki da Turkiyya ke samu.

Minista Simsek ya bayyana kudirin Ankara na ‘dabbaka budaddun manufofin tattain arziki masu dorewa” kamar yadda aka bayyana a baya bayan nan a wasu tarukan kasa da kasa, ciki har da Gawanar Bazara ta IMF-Bankin Duniya

Baya ga tattalin arziki, bangarorin biyu sun kuma tattauna batutun yankunansu.

Jami’an turkiyya sun jaddada bukatar janye takunkumai kan Siriya inda suka kuma jero kokarin diflomasiyya da Turkiyya ke yi wajen ganin an tsagaita wuta a Ukraine.

Manufar cim-ma burin kasuwancin dala biliyan 100

Tattaunawar ta zo a daidai lokacin da alakar tattalin arzikin Amurka da Turkiyya ke habaka, inda dukkan gwamnatocin biyu ke da aniyar habaka kasuwancinsu ya kai na dala biliyan 100.

Masu nazari na sa ran za a samu karin tattaunawar kwararru a watanni masu zuwa don habaga tattaunawar da aka yi a yayin ziyarar ta Washington.

A yayin da Turkiyya ke ci gaba da saisaita kanta a matsayin babbar mai taka rawa a sha’anin tattalin arzikin yanki, habaka alaka da Washington zai zama mai muhimmanci.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#