Dollar

38,7786

0.39 %

Euro

43,8944

0.27 %

Gram Gold

4.147,5900

1.06 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Majalisar ta kuma soke hukuncin da ta yanke kan kudirin doka na soke hukuncin kisa.

Majalisar Wakilan Nijeriya ta janye ƙudurin cire rigar kariya ga Matamakin Shugaban Ƙasa da gwamnoni

Majalisar Wakilai ta sauya matsayarta a karatu na biyu na ƙudirin dokar neman cire rigar kariya ga Mataimakin Shugaban Ƙasa da gwamnonin jihohi da mataimakansu.

An ce an gabatar da ƙudirin dokar ne domin daƙile cin hanci da rashawa da kawar da rashin adalci da kuma ƙara tabbatar da bin gaskiya a ma’aikatun gwamnati.

Sai dai majalisar ta ce ta soke karatu na biyu kan dokar ne saboda an yi watsi da matakin a kan buƙatar gabatar da wasu tanade-tanaden daftarin dokar don yin muhawara.

Majalisar ta kuma soke hukuncin da ta yanke kan ƙudirin doka na soke hukuncin kisa.

Gidan talabijin na Channels TV ya rawaito cewa ƙudurori 42 da ake neman yi wa kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar suka wuce karatu na biyu a zauren majalisar a ranar Laraba, ciki har da na cire rigar kariyar Mataimakin Shugaban Ƙasa da gwamnoni, da mataimakansu.

Kazalika, ƙudirin dokar sauya tanadin kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999, na samar da ofishin Firaminista a matsayin Shugaban Gwamnati da na Shugaban Ƙasa a matsayin shugaban kasa da kuma samar da tsarin yadda za a gudanar da zabe a wadannan ofisoshin, ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar a ranar Alhamis.

Yana daga cikin ƙudurori 32 na gyaran kundin tsarin mulkin kasar da suka wuce karatu na biyu a Majalisar Wakilai a ranar.

Har ila yau, daga cikin ƙudurorin akwai kudirin dokar sauya tanadin kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999, domin samar da wasu kujeru na musamman ga mata a Majalisun Dokokin Ƙasar da Majalisun Jihohi.

Wani kuma shi ne ƙudirin dokar sauya kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999, domin rage tsawon lokaci na tantance al’amuran da suka shafi zabe da kuma samar da kafa kotunan shari’ar gabanin zabe da kuma tsara tsarin dakatar da ɗan majalisar dokokin kasar daga ayyukan majalisa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#