Dollar

38,7786

0.39 %

Euro

43,8944

0.27 %

Gram Gold

4.147,5900

1.06 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Matakin na ƙaƙaba ƙarin haraji kan kayayyakin da aka shigo da su daga ƙetare da ƙasashen uku suka ɗauka yana zuwa ne a daidai lokacin da suke neman ƙarin kuɗaɗe don haɓaka tattalin arzikinsu.

Burkina Faso, Nijar da Mali sun ƙaƙaba haraji kan kayayyakin daga aka kai musu daga ƙasashen ƙetare

Ƙasashen Yammacin Afirka masu maƙwabtaka da juna Mali da Burkina Faso da Nijar sun sanar da sabon haraji na rabin kashi ɗaya cikin 100 kan kayayyakin da aka shigar da su daga ƙetare yayin da suke neman ƙarin kuɗi domin tafiyar da sabon ƙawancen ƙasashe ukun bayan sun fice daga ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka ECOWAS.

Ƙasashen uku da suka kafa ƙawancen ƙasashen Sahel ko AES a shekarar 2023 a matsayin yarjejeniyar tsaro sun bayyana wannan mataki ne a wata sanarwar da suka fitar.

Ƙawancen nasu yanzu tana gab da rikiɗa ta zama ƙawancen tattalin arziƙi inda ake ƙoƙarin samar da fasfo bai ɗaya da ƙarin dangantakar soji.

Ranar juma’a ne dai aka rattaɓa hannu kan harajin kuma dokar za ta fara aiki nan take. Wannan matakin zai shafi dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga wajen ƙasashen uku, amma ba zai haɗa da kayayyakin tallafin jinƙai ba, in ji sanarwar. Wannan zai “samar wa ƙawancen kuɗin tafiyar da ayyukanta,” ba tare da ba da cikakken bayani ba.

Tasiri kan yankin

Wannan matakin zai kawo ƙarshen cinikayya mara tangarɗa a Afirka ta Yamma, inda ƙasashen yankin suka shafe gomman shekaru suka kasance ƙarƙashin inuwar ƙungiyar raya tattalin arziƙin Afirka (ECOWAS), tare da bayyana rabuwa tsakanin ƙasashen uku da ke da kan iyaka da hamadar Sahara da kuma ƙasashe masu faɗa a ji dake bin dimokraɗiyya a kudancinsu kamar Nijeriya da Ghana.

Ƙasashen uku sun fice daga ECOWAS ne cikin ‘yan shekarun nan, inda suka zargi ƙungiyar da gazawa wajen taimaka musu wajen yaƙar ƙungiyoyin ‘yan bindiga  da kuma kawo ƙarshen rashin zaman lafiya.

ECOWAS ta dai ƙaƙaba takunkumin tattalin arziƙi da na siyasa kan ƙasashen uku domin tilasta musu komawa mulkin farar hula ba tare da cim ma wa abun azo a gani ba.

Mali da Burkina Faso da Nijar na fama da hare-haren ƙungiyoyin ‘yan bindiga masu alaƙa da al Qaeda da Daesh, waɗanda suka kashe dubban mutane, tare da tilasta wa miliyoyin mutane tserewa da kuma hana mutane amincewa da zaɓaɓɓun gwamnatocin farar hula da suka sha wahala wajen shawo kan hare-haren daga farko.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#