Hukumar FCC ta nuna damuwa kan yadda aka ce ba a gayyaci wasu masu neman aikin da aka fitar da sunayensu ba a jerin waɗanda suka yi nasara, yayin da wasu da ba a wallafa sunayensu ba suka samu gayyata zuwa horaswar.

Hukumar kwastam ta Nijeriya ta dakatar da horas da sabbin jami’an da ta dauka

Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) ta dakatar da horas da sabbin jami’ai 3,852 da ta dauka aiki, bayan Hukumar Kula da Daidaito a Rabon Mukaman Gwamnati (FCC) ta nuna damuwa kan zargin samun kura-kurai da karya ƙa’idojin rabon mukamai bisa jihohi a tsarin daukar ma’aikatan.

An sanar da dakatarwar ne a ranar Juma’a, bayan tattaunawa tsakanin shugabannin hukumar kwastam da tawagar hukumar FCC.

Hukumar kwastam ta ce an dakatar da ayyukan horaswa a cibiyoyinta biyu domin ba da damar ci gaba da shawarwari da warware matsalolin da suka taso.

Hukumar FCC ta nuna damuwa kan yadda aka ce ba a gayyaci wasu masu neman aikin da aka fitar da sunayensu ba a jerin waɗanda suka yi nasara, yayin da wasu da ba a wallafa sunayensu ba suka samu gayyata zuwa horaswar.

Hukumar ta kuma ce ta samu ƙorafe-ƙorafe daga fiye da masu neman aikin 500, waɗanda suka yi zargin cewa sun kammala dukkan matakan da ake buƙata, ciki har da gwajin lafiya, amma daga baya aka cire su daga cikin waɗanda za a ɗauka.

Hukumar kwastam ta fara aikin ɗaukar ma’aikatan ne a ranar 27 ga Disamban 2024, inda ta sanar da guraben aiki 3,927 a rukuni-rukuni uku. Fiye da mutane 573,000 ne suka nemi aikin, yayin da aka tantance 286,697 domin matakan tantancewa na gaba.

An wallafa jerin sunayen mutane 3,852 da suka yi nasara tsakanin ranakun 28 zuwa 30 ga Yulin 2026. An fara horas da su a ranar 9 ga Oktoba, kafin daga bisani aka sanar da dakatarwar.

Hukumar FCC ta bukaci a gudanar da bincike kan tsarin daukar ma’aikatan, sannan ta ce ta yanke shawarar dakatar da aikin daukar ma’aikatan har sai baba-ta-gani. Ta kuma shigar da ƙara a kotu kan hukumar kwastam saboda kin dakatar da horaswar tun da farko.

Sai dai Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya sake jaddada aniyar hukumar ta yin aiki tare da FCC, domin tabbatar da adalci da gaskiya a tsarin daukar ma’aikata.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: Others

#