A wajen Rohingya, hukunci na tarihi kan kisan kiyashi ya zo tare da amincewar da aka dade ana jira, amma gwagwarmayar adalci, zama dan kasa, da komawa muhallai cikin lumana zuwa kasarsu ba ta kare ba.
Washington, DC — Tsawon kusan shekaru goma kenan, dubban daruruwan Musulman Rohingya ke jiran komawa gidajensu a Myanmar. Da yawa daga cikinsu sun rasa ’yan’uwa, an lalata kauyukansu, yayin da ’ya’yansu ke tasowa a sansanonin ’yan gudun hijira da ke a ƙasashe makwabta.
A ranar Alhamis, Kotun Kasa da Kasa (ICJ) ta yanke hukuncin cewa Myanmar ta aikata kisan kiyashi kan Musulman Rohingya a lokacin mummunan farmakin sojin ƙasar da aka kai a shekarar 2017.
Wannan ne karon farko da babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cewa wata ƙasa tana da alhakin aikata kisan kiyashi. Hukuncin ya zama babbar nasara ta fuskar shari'a ga al'ummar Rohingya, waɗanda suka shafe shekaru suna neman a yi musu adalci.
A wajen al'ummar Rohingya, wannan hukunci na tarihi kan kisan kiyashi ya kasance wani muhimmin ci-gaba.
An yanke hukuncin ne shekaru bakwai bayan da ƙasar Gambia ta shigar da ƙara kan Myanmar a shekarar 2019, inda ta zargi sojojin ƙasar da gudanar da wani shiri da nufin hallaka al'ummar Rohingya baki ɗaya.
Alƙalan kotun sun tabbatar da cewa dakarun Myanmar sun aikata munanan laifuffuka kan fararen hular Rohingya, tare da yin watsi da hujjar ƙasar cewa ayyukan sojinta sun fi mayar da hankali ne kan yaƙar 'yan tawaye.
Kotun ta kuma umarci Myanmar da ta gudanar da bincike tare da hukunta waɗanda ke da hannu a laifukan, ta biya diyya ga waɗanda abin ya shafa, sannan ta samar da yanayin da zai bai wa 'yan gudun hijirar damar komawa ƙasarsu cikin aminci.
Sai dai, mene ne wannan hukunci yake nufi ga al'ummar Rohingya, waɗanda da yawa daga cikin su har yanzu ba su da wata ƙasa da za su kira tasu, kuma suke dogaro da tallafin ƙasashen duniya domin rayuwa?
Jimawa ana jiran adalci
Al'ummar Rohingya sun shafe shekaru da dama suna fuskantar wariya da tsanantawa a Myanmar.
An hana yawancinsu samun takardar zama ’yan ƙasa bisa dokar da aka kafa a shekarar 1982, lamarin da ya hana su cin moriyar yawancin haƙƙoƙin da sauran al'ummomin ƙasar ke da su.
An kuma sanya musu takunkumi kan zirga-zirga, neman ilimi, aikin yi da samun kiwon lafiya, wanda ya ƙara jefa rayuwarsu ta yau da kullum cikin wahala.
Yanayinsu ya ƙara tabarbarewa sosai a watan Agustan 2017, lokacin da sojojin Myanmar suka ƙaddamar da wani farmaki da suka kira aikin share fage a jihar Rakhine, bayan hare-haren da wasu mayakan sa-kai na Rohingya suka kai.
Fiye da mutane 730,000 ne suka tsere zuwa Bangladesh, yayin da rahotanni ke bayyana yadda aka yi kisan kiyashi, fyade da kuma kona kauyuka kurmus.
Daga baya, wani kwamitin binciken gaskiya na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kammala da cewa farmakin sojojin ya ƙunshi ayyukan kisan kiyashi.
A kai a kai, Myanmar ta musanta aikata kisan kiyashi, tana mai cewa dakarunta sun mayar da martani ne kan hare-haren mayaka.
Sai dai Kotun Kasa da Kasa ta (ICJ) ta yi watsi da wannan hujja.
Hukuncin kotun ya tabbatar da cewa munanan laifukan da aka aikata ba sakamakon wani aikin soji kawai ba ne, a'a, ayyuka ne da aka aikata da cikakkiyar niyyar da dokokin ƙasa da ƙasa suka tanada domin tabbatar da aikata kisan kiyashi.
Ga waɗanda suka tsira daga wannan aika-aika, waɗanda suka shafe shekaru suna ba da labarin irin abubuwan da suka faru da su, hukuncin ya zama wata sahihiyar shaida da ta amince da laifukan da aka aikata kan al'ummarsu.
Haka kuma, hukuncin ya tabbatar da alhakin Myanmar a matsayinta na ƙasa, maimakon a bar batun ɗaukar alhaki kawai ga yiwuwar gurfanar da wasu jami'an soji a gaban kotun laifuffuka.
‘Yan Rohingya za su iya komawa gida??
Wataƙila wannan ce tambaya mafi muhimmanci ga 'yan gudun hijirar.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, kimanin 'yan Rohingya miliyan 1.2 ne ke zaune a gundumar Cox's Bazar ta Bangladesh, inda ake samun wasu daga cikin manyan sansanonin 'yan gudun hijira a duniya.
Da yawa daga cikinsu sun kasance a wajen tun shekarar 2017, yayin da wasu kuma suka tsere daga ƙasarsu a lokacin yanayin tsanantawa da ya faru a baya.
Kotun Duniya (ICJ) ta umarci Myanmar da ta samar da hanyoyin da za su ba 'yan gudun hijirar damar komawa ƙasarsu cikin aminci, bisa son ransu da mutuncinsu.
Kotun ta kuma yi kira da a mayar musu da kadarorinsu ko a samar musu da wasu madadinsu, tare da biyan diyya ta wasu hanyoyi ga waɗanda abin ya shafa.
Waɗannan matakai za su iya taimaka wa 'yan gudun hijirar wajen kwato gidaje da filayen da suka rasa a lokacin farmakin sojojin.
Sai dai, hukuncin ba yana nufin za su iya komawa ƙasarsu nan take ba.
Myanmar na fama da rikici tun bayan da sojoji suka ƙwace mulki a shekarar 2021, yayin da sabon faɗan da ake yi a jihar Rakhine ya sake haifar da barazana ga fararen hula.
A halin yanzu, rundunar Arakan Army, wata ƙungiyar mayaƙan ƙabilu da ke yaƙi da sojojin Myanmar, tana da iko da yawancin sassan jihar Rakhine. Wannan kuma ya ƙara dagula batun tantance waɗanda za su iya tabbatar da tsaron 'yan gudun hijirar idan suka koma.
Ga iyalan Rohingya, komawa ƙasarsu ba tare da samun izinin zama 'yan ƙasa ba, 'yancin zirga-zirga da kariya daga sake fuskantar tashin hankali ba, na iya nufin komawa cikin irin yanayin da ya tilasta musu barin ƙasarsu tun farko.
Hukuncin kotun ya samar da tubalin doka da za su dogara da shi wajen neman a mayar da su ƙasarsu. Sai dai aiwatar da hakan zai buƙaci sauye-sauye a fannin siyasa da tsaro a cikin Myanmar.
Ko Myammar za ta biya diyya?
Kotun ta umarci Myanmar da ta biya diyya ga waɗanda kisan kiyashin ya shafa.
Wannan diyyar na iya haɗawa da biyan kuɗaɗen diyya, mayar da kadarori ko samar da wasu madadinsu, da kuma tallafa wa mutanen da suka fuskanci raunuka na jiki da na ƙwaƙwalwa.
Har yanzu dai ba a tantance adadin kuɗin diyyar da za a biya ba.
Ga iyalan da suka rasa gidajensu, gonakinsu da hanyoyin samun abin rayuwarsu, wannan diyyar na iya zama wani muhimmin mataki wajen sake gina rayuwarsu.
Sai dai, biyan diyya kaɗai ba zai iya maye gurbin asarar ’yan uwa ko shekarun da suka shafe suna gudun hijira ba.
Akwai kuma batun yadda za a tabbatar da aiwatar da hukuncin.
Hukuncin Kotun Kasa da Kasa (ICJ) na da cikakken ƙarfi a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, kuma babu damar ɗaukaka ƙara a kansa. Sai dai kotun ba ta da rundunar ’yan sanda da za ta tilasta wa gwamnatoci bin umarninta.
Saboda haka, matakin da Myanmar za ta ɗauka zai kasance mai matuƙar muhimmanci, tare da irin ƙoƙarin da sauran ƙasashe da hukumomin ƙasa da ƙasa za su yi wajen matsa mata lamba domin tabbatar da aiwatar da hukuncin.
Ko masu alhakin rikicin za su fuskanci hukunci?
Hukuncin Kotun ICJ ya ɗora wa Myanmar alhakin aikata laifuffukan da suka saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, amma bai yanke wa manyan kwamandojin sojin ƙasar hukuncin laifi ba.
Dalilin hakan shi ne, kotun tana sauraron rikice-rikice tsakanin ƙasashe ne, ba shari'o'in laifuffuka da ake tuhumar mutane ɗaiɗaiku ba.
Sai dai ana ci gaba da gudanar da wasu shari'o'i daban ta hannun Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC), wadda ke bincike tare da gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata manyan laifuffuka na ƙasa da ƙasa.
A shekarar 2024, mai gabatar da ƙara na ICC ya nemi a bayar da sammacin kama shugaban sojojin Myanmar, Min Aung Hlaing, bisa zargin aikata laifuffukan cin zarafin bil'adama da ke da alaƙa da tilasta wa al'ummar Rohingya barin gidajensu.
Hukuncin ICJ na iya ƙarfafa kiraye-kirayen neman a hukunta mutanen da ke da hannu a waɗannan laifuka, duk da cewa ba ya nufin kai tsaye za a yanke musu hukuncin laifi ko a kama su.
Kotun ta kuma umarci Myanmar da ta gudanar da bincike tare da hukunta waɗanda ke da alhakin aikata waɗannan munanan laifuffuka.
Ga waɗanda suka tsira daga wannan aika-aika a cikin al'ummar Rohingya, wannan bambanci yana da muhimmanci. Tabbatar da cewa wata ƙasa ce ke da alhakin aikata laifuffuka babban mataki ne, amma da yawa daga cikinsu suna son ganin an gurfanar da jami'an soji da sauran waɗanda suka taka rawa a wannan tashin hankali domin su fuskanci hukunci.
Me ya sauya ga masu neman mafaka a Bangladesh?
A yanzu haka, da wuya hukuncin kotun ya kawo wani gagarumin sauyi a rayuwar yau da kullum ta 'yan gudun hijirar.
Iyalan na ci gaba da zama a sansanonin 'yan gudun hijira masu cunkoso, inda damar samun ilimi, aikin yi da kiwon lafiya take da ƙaranci.
Da yawa daga cikin su suna dogaro da ƙungiyoyin agaji wajen samun abinci da sauran muhimman abubuwan buƙatun rayuwa.
Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) ta sha bayyana ƙalubalen da 'yan gudun hijirar Rohingya ke fuskanta, ciki har da dogaro da tallafin jinƙai da kuma buƙatar samar da damar komawa ƙasarsu cikin aminci da son ransu.
Rashin isassun kuɗaɗen tallafi ya ƙara tsananta matsalolinsu, yayin da rashin tsaro da ƙarancin damar samun abin yi suka sa wasu 'yan gudun hijirar shiga tafiye-tafiyen teku masu haɗari domin neman rayuwa mafi kyau.
Hukuncin Kotun Kasa da Kasa (ICJ) ba ya nufin za a samar musu da ƙarin tallafin jinƙai kai tsaye, ko kuma a magance matsalolin da ake fuskanta a sansanonin.
Sai dai, yana iya ƙara matsin lambar ƙasashen duniya kan Myanmar, tare da ƙarfafa gwamnatoci su ƙara mayar da hankali kan matsalar al'ummar Rohingya.
Haka kuma, hukuncin ya ƙara ƙarfafa hujjar cewa bai kamata a tilasta wa 'yan gudun hijirar komawa ƙasarsu ba har sai an tabbatar da cewa yanayin tsaro ya inganta, kuma ana kiyaye haƙƙoƙinsu
Me zai faru a nan gaba?
Hukuncin kotun na ƙarshe ne, kuma yana da cikakken ƙarfi a ƙarƙashin doka bisa Mataki na 59 na Dokar Kafa Kotun da kuma Mataki na 94 (1) na Yarjejeniya ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ana buƙatar Myanmar ta bi umarnin kotun, ciki har da gudanar da bincike kan laifukan da aka aikata, biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa da kuma samar da damar komawa ga 'yan gudun hijira cikin aminci.
Idan ta gaza yin hakan, ƙasar Gambia za ta iya neman a ɗauki wasu matakai a matakin ƙasa da ƙasa, ciki har da kai batun gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sai dai, bambance-bambancen ra'ayi na siyasa tsakanin manyan ƙasashen duniya na iya sanya aiwatar da hukuncin ya zama mai wahala.
Hukuncin na iya kuma yin tasiri ga sauran shari'o'in da ake saurara a gaban Kotun Kasa da Kasar kan zargin kisan kiyashi, ciki har da ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra'ila dangane da Gaza, musamman wajen yadda alƙalai ke tantance hujjojin da ke nuna niyyar hallaka wata al'umma da dokokin ƙasa da ƙasa ke ba kariya.
Ga al'ummar Rohingya, hukuncin da aka yanke ranar Alhamis wani muhimmin ci gaba ne bayan shekaru da dama na jira.
Babbar kotun duniya ta tabbatar a hukumance cewa an yi wa al'ummarsu kisan kiyashi, kuma Myanmar ce ke da alhakin hakan.
Sai dai, manyan tambayoyin da suka shafi makomarsu har yanzu ba su samu amsa ba.
Hukuncin ya buɗe wata hanya ta neman adalci, amma ainihin muhimmancinsa zai dogara ne da abin da zai faru bayan an bar zauren kotun.
Ga al'ummar Rohingya, babban burinsu shi ne su koma mahaifarsu, su rayu ba tare da tsoro ba, kuma su samu haƙƙoƙi iri ɗaya da sauran 'yan ƙasar.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Reuters (Wire)

