Da yake magana gabanin wani taron koli na ƙungiyar APEC ta kasashe uku a China, Trump ya ce Amurka ta raunana karfin sojin Iran matuka, kuma tana da cikakken iko da mashigar ruwan Hormuz

Trump ya ce Amurka ba ta buƙatar taimakon China ko Rasha wajen kawo ƙarshen yaƙin da take yi da Iran

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Washington ba ta bukatar taimakon China ko Rasha wajen kawo karshen yakin da take yi da Iran, yana mai cewa dakarun Amurka sun yi wa karfin sojin Tehran mummunar illa.

Da yake magana gabanin wani taron koli na ƙungiyar APEC ta kasashe uku a China, Trump ya ce Amurka ta raunana karfin sojin Iran matuka, kuma tana da cikakken iko da mashigar ruwan Hormuz.

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar Fox News a birnin Shenzhen na China a ranar Alhamis, jim kadan kafin ganawarsa ta kasashe uku da Shugaban China Xi Jinping da Shugaban Rasha Vladimir Putin.

"Ba ma bukatar taimakon kowa. Mun karya karfin rundunar sojin ruwan Iran, mun karya karfin rundunar sojin sama, sannan mun lalata na'urorinta na kariya daga hare-haren sama," in ji Trump.

Ya kuma yi ikirarin cewa yawan makamai masu linzami da Iran ke da su ya ragu zuwa kusan kashi 12 zuwa 13 cikin 100 daga na baya, yana mai cewa Tehran na son cim ma yarjejeniya da Amurka.

Yana ƙara da cewa "saboda haka, ba na bukatar taimako, kuma ba zan je neman taimakon kowa ba."

Trump ya ce sojojin Amurka na da cikakken iko kan mashigar ruwan Hormuz, yana mai cewa China da Rasha sun nuna kyakkyawar mu'amala da Washington, kuma sun ƙi tura jiragen yakin ruwansu zuwa yankunan da ake takaddama a kansu.

Cim ma yarjejeniya mai dorewa da Iran

Da yake magana kan tattaunawar da ake yi da Tehran, Trump ya yi ikirarin cewa shugabannin Iran na neman a cim ma matsaya, amma shi yana son yarjejeniyar da za ta dore na dogon lokaci.

"Zan kawo karshen lamarin nan ba da jimawa ba. Ina nufin, ko ta wace hanya, za mu kawo karshensa," in ji shi.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ganawa da Xi Jinping da Vladimir Putin a lokaci guda za ta amfani Amurka, Trump ya ce hakan na da muhimmanci ne saboda kasashen biyu suna aiki tare kuma suna da kyakkyawar alaka.

Ya zargi tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da hada kan China da Rasha saboda batun makamashi, yana mai cewa China na matukar bukatar makamashi, yayin da Rasha ke da dumbin albarkatun makamashi.

Trump ya kara da cewa yana ganin Amurka na samun nasara a halin da ake ciki, yana mai cewa shugabannin kasashen biyu suna kaunarsa.

Game da rahotannin leken asiri da ke zargin Iran da shirin amfani da makamai masu guda wajen kai wa Washington DC hari, Trump ya ce akwai alamun Iran na nazarin amfani da makamai masu guba.

Yana mai cewa, "akwai alamun Iran na duba yiwuwar amfani da iskar gas da kuma makamai masu guda, Idan hakan ta faru, za mu murkushe su gaba daya."

Trump ya kuma musanta cewa wasu mambobin majalisarsa da ke zaune a sansanonin sojin Amurka sun koma can ne saboda barazanar da Iran ke yi.

Wadannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada sakamakon yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran a ranar 28 ga watan Fabrairu, wanda ya janyo martanin hare-haren ramuwar gayya daga Tehran kan Isra'ila da kasashen yankin Gulf da ke karbar sansanonin sojin Amurka.

An rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a watan Yuni, amma ba a aiwatar da ita gaba daya ba sakamakon sabanin da aka samu kan tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar ruwan Hormuz. An kuma ci gaba da samun arangama lokaci-lokaci tun daga watan Yuli.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: Reuters

#