Masu aikin ceto na ci gaba da neman waɗanda suka tsira bayan wani kwale-kwale cike da fasinjoji da ke kan hanyarsa ta zuwa jana’iza ya kife a Jihar Bayelsa da ke kudancin Nijeriya, inda ake fargabar mutuwar mutane da dama.

Lamarin ya faru ne a wani yanki kusa da garin Ukubie, a ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu, yayin da kwale-kwalen ke ɗauke da fasinjoji zuwa jana’iza, a cewar mazauna yankin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Bayelsa, Musa Mohammed, ya ce an tura jami’an rundunar ’yansandan ruwa domin taimaka wa ayyukan ceto.
Sai dai har yanzu ’yansandan ba su bayyana adadin mutanen da suka mutu, waɗanda aka ceto ko kuma waɗanda ake nema ba.
Wata shaidar gani da ido, Sophie Igoniwari, ta ce an cika kwale-kwalen maƙil bayan turereniyar da aka yi yayin shiga kwale-kwalen kafin ya taso daga Anyama Ijaw. Ta ƙara da cewa an ga an fito da wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa zuwa gabar ruwa bayan kwale-kwalen ya kife jim kaɗan da tashinsa.
Haɗurran kwale-kwale sun zama ruwan dare a hanyoyin ruwa na cikin gida a Nijeriya, musamman a yankunan da ke kewaye da ruwa, inda ake yawan samun cunkoso da kuma rashin bin ƙa’idojin tsaro.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Reuters (Wire)