Shugaba Bassirou Diomaye Faye na takun saƙa da Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda jam’iyyar adawa ta Pastef ke da rinjayen kujeru kuma ta ƙi amincewa da matakan kasafin kuɗin da shugaban ƙasar ya gabatar.
Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya bayar da umarnin fara aiki da dokar kasafin kuɗi ta hanyar rattaba hannu kan wata doka, duk da cewa majalisar dokokin ƙasar ta ƙi amincewa da ita. Ana ganin dokar na da muhimmanci wajen farfaɗo da harkokin kuɗin gwamnati, a daidai lokacin da ƙasar ke kammala shirin neman tallafin kuɗi daga Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF).
Ofishin shugaban ƙasar a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ya bayyana cewa Faye “ya yanke shawarar sanya dokar gyaran kasafin kuɗin shekarar 2026 ta fara aiki”, matakin da ya ɗauka ba tare da amincewar majalisa ba.
Senegal, wadda ke fama da dimbin basussuka, na cikin wani yanayi na rashin jituwa tsakanin ɓangarorin siyasa da kuma takaddamar kasafin kuɗi da ba a taɓa ganin irinta ba. Faye na takun saƙa da Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda jam’iyyar adawa ta Pastef ke da rinjayen kujeru kuma ta ƙi amincewa da matakan kasafin kuɗin da shugaban ƙasar ya gabatar.
Shugaban jam’iyyar Pastef, Ousmane Sonko, wanda a baya amininsa ne amma daga bisani suka zama abokan hamayyar siyasa, ya ƙi amincewa da sake fasalin basussukan ƙasar, wanda hakan na daga cikin sharuddan rancen IMF.
A baya ya bayyana wannan mataki a matsayin “abin kunya” da zai iya tauye ikon Senegal na cin gashin kanta.
‘Babban kuskure’
Duk da cewa jam'iyyar Pastef ba ta mayar da martani kan matakin shugaban ƙasar ba, wani fitaccen ɗan majalisar jam'iyyar, Amadou Ba, ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa shugaban ƙasar yana aikata "babban kuskure", yana mai cewa ba shi da ‘‘ikon sanya kasafin kuɗin da majalisa ta ƙi amincewa da shi ya zama doka.’’
A watan Satumba, Senegal ta sanar da cim ma yarjejeniyar shirin bashi na dala biliyan 2.2 da Asusun Ba da Lamuni na Duniya, domin taimakawa wajen daidaita harkokin kuɗin ƙasar.
Sai dai har yanzu hukumar gudanarwar IMF ba ta sanar da amincewa da shirin ba, kuma bayar da tallafin ya ta'allaka ne da cika wasu sharudda.
Sabon kasafin kuɗin shekarar 2026 da kuma daftarin kasafin shekarar 2027 na daga cikin muhimman matakan da ake sa ran za su taimaka wajen magance matsalar dimbin basussukan Senegal.
A daya hannun kuma, shugaban babbar ƙungiyar ƙwadago ta CNTS-FC, Cheikh Diop, ya yi maraba da matakin shugaban ƙasar, yana mai cewa ya zo a matsayin wani babban sauƙi ga ma'aikata.
Ya ce matakin zai ba gwamnati damar biyan basussukan cikin gida, waɗanda ke zama ‘‘wani babban nauyi ga rayuwar ma'aikata, da tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya da kuma ɓangaren gine-gine da ayyukan raya ƙasa.’’
Tasirin matakin ga tattalin arziki
Gwamnatin Senegal ta yi gargaɗin cewa rashin amincewa da sabon kasafin kuɗin na iya kawo cikas ga samar da wutar lantarki, da biyan basussukan da ake bin gwamnati daga kamfanoni da kuma biyan albashin malaman makaranta da aka jinkirta.
Matakin aiwatar da kasafin kuɗin ta hanyar ƙarfin ikon mulkin shugaban ƙasa ya zo ne a daidai lokacin da ake sa ran majalisar dokokin ƙasar za ta sake ƙin amincewa da kasafin kuɗin da gwamnati ta gabatar na shekarar 2027.
'Yan majalisar sun ƙi amincewa da wasu sassan daftarin kasafin kuɗin yayin zaman majalisa na ranar Laraba, bayan irin wannan mataki da kwamitocin majalisar suka ɗauka a makon da ya wuce.
A makon da ya gabata, IMF ta ce a shirye take ta tattauna da masu ruwa da tsaki a Senegal kan sharuddan shirin rage nauyin basussukan ƙasar, yayin da takaddamar siyasa ke barazana ga shirin.
Ci gaba da shirin zuwa mataki na gaba "ya dogara ne wajen kammala matakan da aka amince da su kan tsarin kasafin kuɗi," kamar yadda mai magana da yawun IMF, Julie Kozack,ta bayyana a wani taron manema labarai.
A ƙarshen shekarar 2024, an kiyasta cewa yawan basussukan gwamnatin Senegal ya kai kashi 132 cikin 100 na jimillar ma’aunin tattalin arzikin ƙasar na (GDP).
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: AFP (Wire)

