Atiku Abubakar ya yi gargaɗin cewa idan ba a samar da isassun matakan kariya ba, fasahar AI na iya jinkirta ko nuna sakamakon sahihin zaɓe a matsayin wanda ake zargi da matsala.
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, kuma ɗantakarar shugabancin ƙasar ƙarƙashin Jam’iyyar ADC Atiku Abubakar, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) da ta fayyace tsarin fasaharta ta AI da take shirin amfani da shi domin gudanar da bincike mai zaman kansa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Atiku, ta bakin Daraktan Sadarwa da Dabarun Yaɗa Labaransa, Phrank Shaibu, ya ce ya aika da koke ga Shugaban INEC a madadin Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da sauran masu ruwa da tsaki, inda ya nemi a yi gaskiya wajen bayyana yadda tsarin ke aiki, tare da gudanar da bincike mai zaman kansa da kuma samar da ƙa’idojin sa ido na ɗan’adam.
Wannan buƙata na zuwa ne bayan INEC ta sanar da shirin haɗa fasahar AI da tsarin sarrafa takardu ta hanyar na’ura wajen tantance sakamakon zaɓe a matakin mazaɓu, ta hanyar tsarin Data Verification and Authentication System (DIVAS) da kuma shafin INEC Result Viewing (IReV).
Atiku ya yi gargaɗin cewa idan ba a samar da isassun matakan kariya ba, fasahar na iya jinkirta ko nuna sakamakon zaɓe na gaskiya a matsayin wanda ake zargi da matsala, sakamakon rashin ingancin hoton takarda, ko rubutun hannu ko kuma wasu matsalolin fasaha.
Ya bukaci INEC da ta bayyana lambar sirrin tsarin wato (source code), da bayanan da aka yi amfani da su wajen horas da shi, da ka’idojin gudanar da aikinsa da kuma sunayen wadanda suka kirkire shi da kamfanonin fasahar da ke da hannu a aikin.
Haka kuma, ya bukaci kwararru kan tsaron yanar gizo masu zaman kansu, da wakilan jam’iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula da su gudanar da bincike kan tsarin kafin atisayen gwajin tantance masu kada kuri’a a fadin kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 28 ga Nuwamba, 2026.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma jaddada cewa, ya kamata fasahar AI ta zama wani kayan aiki na taimakawa wajen gudanar da ayyukan zaben, karkashin kulawar ɗan Adam, yana mai gargadin cewa bai kamata a ba shi ikon sauya sakamakon zabe, goge shi ko hana shigar da shi har abada ba.
Ya kuma bukaci INEC da ta samar da wani bayyanannen tsari na sake duba sakamakon da na’urar ta nuna yana da matsala, tare da bai wa jam’iyyun siyasa damar sa ido kan yadda ake shigar da sakamakon zabe a kan lokaci.
Kazalika, Atiku ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa da ta gayyaci jami’an INEC domin su yi bayani kan matakan kariya da tsarin binciken fasahar, tare da bukatar masu sa ido kan zabe su yi bincike sosai kan yadda ake shigar da sakamako ta hanyar na’ura.
Haka kuma, ya ce dole ne ‘yan Nijeriya su samu damar tabbatar da cewa sakamakon da aka tattara a rumfunan zabe ya yi daidai da wanda aka shigar a shafukan hukumar ta yanar gizo.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: TRT Afrika Hausa

