Ministan Harkokin Cikin Gida na Nijeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce ana sa ran kammala ginin tare da ƙaddamar da cibiyar a watan Mayun 2027, matakin da zai rage dogaron Nijeriya ga kamfanonin ƙasashen waje.
Nijeriya na shirin fara buga takardun fasfo a cikin gida daga watan Mayun 2027, bayan kammala gina wata cibiyar kera fasfo ta dala miliyan 70 a babban birnin ƙasar, Abuja.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin bikin ƙaddamar da ginin Cibiyar Buga Fasfo ta Ƙasa.
Ya ce ana sa ran kammala ginin tare da ƙaddamar da cibiyar a watan Mayun 2027, matakin da zai rage dogaron Nijeriya ga kamfanonin ƙasashen waje, tare da kare ta daga matsalolin da ka iya tasowa a hanyoyin samar da kayayyaki daga ƙasashen waje.
Tunji-Ojo ya ce ana gina cibiyar ne tare da haɗin gwiwar kamfanin Iris Smart Technologies, ba tare da gwamnati ta kashe kuɗi kai tsaye wajen aikin ba.
A cewarsa, cibiyar za ta fara da ƙarfin samar da fasfo na zamani miliyan shida a duk shekara, tare da shirin ƙara adadin zuwa miliyan 10.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu Nijeriya na buƙatar fasfo tsakanin miliyan 1.8 zuwa miliyan biyu a duk shekara, kuma daga baya cibiyar za ta iya samar da fasfo ga sauran ƙasashen Afirka ta Yamma da mambobin Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).
Ministan ya bayyana aikin a matsayin wani babban mataki na ƙarfafa ƙarfin Nijeriya wajen samar da ingantattun fasfo na zamani a cikin gida.
Tun da farko, Babbar Kwanturola-Janar ta Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, Kemi Nana Nandap, ta ce ’yan ƙasar sun shafe shekaru suna fuskantar ƙarancin takardun fasfo da kuma dogon lokacin jira kafin samun su.
Ta ce sabuwar cibiyar za ta ƙarfafa ikon ƙasar kan samar da fasfo, inganta wadatar su da kuma inganta ayyukan da ake yi wa ’yan ƙasa.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Others

