Fidan ya jaddada cewa Libya ta kasance wani muhimmin ɓangare ga manufar Turkiyya a gabashin Bahar Rum, wadda ke da niyyar samar da zaman lafiya da wadata.

Minsitan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan ya jaddada goyon bayan Ankara ga haɗin kan Libya

Minsitan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce Ankara za ta ci gaba da ƙarfafa tattaunawa tsakanin dukkan ɓangarorin Libya a wani ɓangare na ƙoƙarinta na tallafa wa haɗin kan siyasar ƙasar da dunƙulewar ƙasar da kuma zaman lafiya.

Da yake magana a gaban kwamitin dindindin na Tsari da Kasafin Kuɗi na Majalisar Dokokin Turkiyya a ranar Alhamis, Fidan ya jaddada cewa Libya ta kasance wani muhimmin ɓangare ga manufar Turkiyya a gabashin Bahar Rum, wadda ke da niyyar samar da zaman lafiya da wadata.

Fidan ya ce Turkiyya na ci gaba da ƙoƙarin inganta tattaunawa tsakanin ɓangarorin siyasa a Libya bisa tsarin manufofinta na “Libya Ɗaya”, tare da yabawa da amincewa da yarjejeniyar harkokin teku da Libya da Turkiyya suka kulla a baya-bayan nan.

Ya ce, “Amincewa da ƙuri’ar bai ɗaya da Majalisar Wakilan Libya da ke yankin gabashin ƙasar ta yi a ranar 20 ga Oktoba da yarjejeniyar fahimtar juna kan fayyace iyakokin ikon teku, wadda ta fara aiki tsakanin ƙasashenmu tun daga shekarar 2019, na nuna cewa manufofinmu masu tushe kan ƙa’idoji suna haifar da sakamako.”

Fidan ya kuma yi magana kan dangantakar Turkiyya da Masar. Ya ce alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu, waɗanda ke daga cikin manyan ƙasashen da ke da tasiri a Gabashin Bahar Rum da Arewacin Afirka, na ci gaba a matakin dabarun haɗin gwiwa, kuma an ƙara ƙarfafa ta a shekarar 2026 ta hanyar ganawar manyan jami’ai.

Ya ce, “Za mu ci gaba da inganta dangantakarmu da Masar bisa mutunta juna da muradun bai ɗaya, ta yadda hakan zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da bunƙasar yankin.”

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: AA

#