Kane ya ji raunin ne mintuna 20 bayan fara wasan da Bayern Munich ta tashi kunnen doki 1-1 da Cologne a filin wasanta, a gasar Bundesliga a ranar Juma’a. Daga baya ƙungiyar ta tabbatar da cewa kyaftin ɗin tawagar Ingila ya samu raunin a idon sawunsa.

Harry Kane: Ɗanƙwallon Bayern Munich ya yi alƙawarin komawa wasa bayan an yi masa tiyata a idon sawu

Fitaccen ɗan wasan gaba na Bayern Munich, Harry Kane, ya yi alkawarin komawa domin taimaka wa ƙungiyarsa a muhimman wasannin ƙarshen kakar wasa, bayan an yi masa tiyatar raunin idon sawun ƙafar hagunsa a ranar Asabar.

Kane ya ji raunin ne mintuna 20 bayan fara wasan da Bayern Munich ta tashi kunnen doki 1-1 da Cologne a filin wasanta, a gasar Bundesliga a ranar Juma’a. Daga baya ƙungiyar ta tabbatar da cewa kyaftin ɗin tawagar Ingila ya samu raunin a idon sawunsa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, Bayern ta ce Kane, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or, an yi nasarar kammala tiyatar da aka yi masa a ƙafar hagunsa.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ɗan wasan mai shekaru 33 zai fara shirin murmurewa, inda ake sa ran raunin zai hana shi buga wasa na tsawon watanni uku zuwa huɗu.

Kane ya wallafa hotonsa daga gadon asibiti a shafukan sada zumunta, inda ya bayyana cewa zai yi aiki tuƙuru domin dawowa cikin ƙoshin lafiya a wannan kakar.

“Rayuwa tana cike da farin ciki da ƙalubale! A bayyane yake cewa na ji matuƙar takaici da wannan rauni, amma kamar yadda aka saba, wannan wata dama ce ta nuna juriyata da inganta kaina yayin da muke shirin shiga shekarar 2027,” kamar yadda Kane ya bayyana.

“Zan dawo cikin ƙoshin lafiya da shirin tunkarar muhimman wasannin ƙarshen kakar wasa,” kamar yadda Kane ya ƙara da cewa.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: Reuters (Wire)

#