Iran ta yi nuni kan mamayar da Amurka ta kai wa Iraki a shekarar 2003, yayin da take ƙaryata zargin Washington na cewa Tehran na iya ƙera makaman yaƙi masu guda, tana mai gargaɗin cewa Amurka na sake maimaita irin dabarun yaudarar da ta yi a baya.

Iran ta ce Amurka ta maimaita ƙaryar da ta yi wa Iraƙi, a zarginta na mallakar makamai masu guba

Iran ta ƙaryata zargin Amurka na cewa tana iya ƙera makaman yaƙin halittu ko sinadarai masu guba, inda ta kwatanta zargin da Washington ta yi wa Iraki kan mallakar makaman kare dangi gabanin mamayar ƙasar a shekarar 2003.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya yi wata tambaya a shafinsa na X kan ko ana tsammanin ƙasashen duniya za su manta da jawabin da tsohon sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya gabatar a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya a watan Fabrairun 2003, inda ya yi ikirarin tabbatar da cewa Baghdad tana da makaman kare dangi.

An yi amfani da waɗannan zarge-zarge wajen ba da hujjar mamayar da Amurka da ƙawayenta suka jagoranta a Iraki a watan Maris na shekarar 2003, duk da cewa daga baya ba a tabbatar da hujjojin zargin ba.

Baqaei ya yi zaton jama’a za su yi saurin mantawa da abubuwan dasuka faru ne, kamar wani kifin Dory da aka fi sani da saurin mantuwa, a fim ɗin zane mai motsi na Finding Nemo.

"Da alama ana sake sa ran duniya za ta kamu da cutar mantuwa, kamar kifin Dory mai saurin mantuwa a fim ɗin Finding Nemo," in ji shi.

Ya ce zarge-zargen da aka yi wa Iraki sun taimaka wajen samun goyon bayan jama'a ga mamayar ƙasar, wadda ta haifar da mummunan sakamako ga al'ummar Iraki, da yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya, har ma da al'ummar Amurka.

Tehran ta gargaɗi Amurka kan maimaita irin hujjar da ta bayar wajen mamayar Iraki

"Yanzu kuma muna fuskantar wasu sabbin zarge-zarge masu tayar da hankali," a cewar Baqaei, yana mai bayyana cewa waɗannan zarge-zarge da irin abin da ya kira "tsohuwar dabarar yaudara".

Haka kuma, a tambayi ko ƙasashen duniya sun koyi darasi daga illolin yaƙin shekarar 2003, ko kuma za su sake barin a yaudare su ta wannan hanya.

Kalamansa sun biyo bayan zantawar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi da tashar Fox News a ranar Laraba, inda ya ce akwai alamu da ke nuna Iran na ƙoƙarin ƙera makamai masu guba, bayan lalacewar shirinta na nukiliya.

A baya dai Trump ya sha bayyana zargin barazanar shirin nukiliyar Iran a matsayin ɗaya daga cikin hujjojin da suka sa Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da yaƙi kan Tehran a watan Fabrairu.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: AP

#