Sport
Dollar
42,9664
0.08 %Euro
50,6224
0.03 %Gram Gold
5.966,2100
0.22 %Quarter Gold
10.158,3200
0 %Silver
98,9400
0.85 %Anthony Joshua, mai shekaru 36, yana tafiya ne shi da abokansa a cikin mota ƙirar Lexus Jeep a kan hanyar Lagos zuwa Ibadan, inda motar ta yi karo da wata babbar mota da aka ajiye a gefen hanya.
An sallami gwarzon ɗan damben boksin ɗan ƙasar Birtaniya kuma ɗan asalin Nijeriya Anthony Joshua daga asibiti bayan ya gamu da mummunan hatsarin mota a Jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Nijeriya.
Anthony Joshua, mai shekaru 36, yana tafiya ne shi da abokansa a cikin mota ƙirar Lexus Jeep a kan hanyar Lagos zuwa Ibadan, inda motar ta yi karo da wata babbar mota da aka ajiye a gefen hanya.
Abokan nasa biyu Lateef Ayodele and Cina Gami sun rasu sakamakon hatsarin, ko da yake Joshua ya tsallake rijiya da baya inda ya samu raunuka.
Wata sanarwa da gwamnatin Jihar Ogun ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba da ta ce an sallami Joshua ne da yammacin ranar.
"An sallami Anthony Joshua daga asibiti da wannan la'asar ɗin bayan likitoci sun tabbatar cewa zai iya tafiya gida domin ya murmure ko da yake yana cike da matuƙar alhini na rashin aminansa biyu,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa Anthony da mahaifiyarsa sun je gidan da aka ajiye gawawwakin abokansa a birnin Lagos domin su yi musu bankwana a "yayin da ake shirin kwashe su domin fitar da su daga ƙasar nan gaba da wannan la'asar."
Sanarwar ta ce gwamnatin Jihar Ogun da ta Jihar Lagos sun jaddada miƙa saƙon ta’aziyyarsu ga iyalan Lateef Ayodele da Cina Gami waɗanda suka rasu “a hatsarin motar da Anthony Joshua ya yi ranar 29 ga watan Disamban 2025.”
Tun da farko shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya nuna alhininsa game da aukuwar hatsarin, sanna ya bayyana cewa ya yi magana da Anthony Joshua inda ya ƙarfafe shi tare da yin alhini a gare shi.
Joshua ya je Jihar Ogun ne inda yake da dangi a garin Sagamu yayin da ya samu hatsarin na mota.
Ɗanwasan dai ya kai ziyara Nijeriya ne domin hutun ƙarshen shekara, ‘yan kwanaki bayan ya yi nasara kan Jake Paul a birnin Miami na Amurka ranar 19 ga Disamba.
Comments
No comments Yet
Comment