Sport
Dollar
40,6705
0.08 %Euro
46,4448
-0.12 %Gram Gold
4.315,3200
0.37 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Furqan Hameed, mawallafin littafin, ya bayyana Shugaban Turkiyya Erdogan a matsayin “fitaccen shugaba” wanda shugabancinsa ya yi muhimmin tasiri a Turkiyya da faɗin duniya Musulmi.
An ƙaddamar da wani sabon littafi da ya yaba da ƙarfin faɗa-a-ji na Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a Duniyar Musulmi ranar Litinin, inda manyan jami’an Pakistan ke yaba masa a matsayin wata alama ta ƙarfin zuciya da kuma haɗin kan Musulman Duniya.
Ɗan jarida kuma marubuci Furqan Hameed ne ya rubuta littafin mai suna Recep Tayyip Erdogan – Tiger of the Islamic World.
Bikin ƙaddamar littanin, wanda aka yi a babban birnin Pakistani, ya samu halarcin ministan watsa labarai Ataullah Tarar, wanda ya bayyana Erdogan a matsayin “shugaban duniya wanda ayyukansa ke nuna jajircewa wajen bin gaskiya.”
“Wannan littafin jinjina ne ga wani shugaba na duniyar Musulmi mai hangen nesa,” in ji Tarar, yana mai bayyana yadda Erdogan ya nuna goyon baya ga Falasɗinu da kuma ayyukan jinƙai a fagen duniya irin MDD da taron D-8 da kuma ƙungiyar Haɗin kai ta Shanghai.
'Shugabancin da ya mayar da hankali kan mutane da juriyar siyasa'
Tarar ya ce shugabancin Erdogan, tun daga farko a matsayin Magajin Garin Istanbul zuwa matsayinsa na shugaban ƙasa da shugaban jam’iyyar AK Party, ya kwatanta shugabancin da ya mayar da hankali kan mutane da kuma juriya ta siyasa.
“Shugaba ne na mutane kuma ƙwararren mai gudanarwa wanda salon shugabancinsa na ci gaba da kasancewa abin sha’awa a faɗin duniya,” in ji Tarar.
Ministan na Pakistani ya yaba wa muryar Erdogan “wadda ba ta sauyawa” a kan [goyon bayan] Gaza, yana mai bayyanata a matsayar manuniya kan daɗaɗɗiyar jajircewar Turkiyya ga Duniyar Musulunci. Ya kuma bayyana dangantakar da ke tsakanin Pakistan da Turkiyya wadda ta samo asali daga haɗin kai na da can tun lokacin kalifanci.
“Dangantakarmu ba za a iya yanke ta ba, an gina ta ne kan tausayi da juriya da kuma girmamawa ga juna,” in ji shi, yana mai bayyana tsarin sufurin cikin birnin Lahore a matsayin wani misali na hadin kai mai ma’ana.
‘Fitaccen Shugaba’
Marubuci Furqan Hameed ya ce littafin ya bi diddigin tarihin Erdogan daga siyasa na cikin gida zuwa inda ya zama sananne a duniya, yana mai bayya shi a matsayin “fitaccen shugaba” wanda shugabancinsa ke tasiri nesa da Turkiyya.
“Fafutukarsa da kuma hangen nesansa ba a kan Turkiyya kawai suke tasiri ba, amma suna samun karɓuwa a Duniyar Musulmi,” in ji Hameed.
Ƙaddamar da littafin ya kansace jinjina na adabi da sake jaddada dangantaka mai ƙara ƙarfi tsakanin Pakistan da Turkiyya, inda aka bayyana Erdogan ba a matsayin shugaba na ƙasa kawai bai, amma a matsayin wanda ake ƙauna a ƙasashen duniya.
Comments
No comments Yet
Comment