Sport
Dollar
40,7015
0.02 %Euro
47,2204
1.43 %Gram Gold
4.394,9300
2.22 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Gwamnatin Ghana ta ce hanyoyin ƙasar da dama sun lalace sakamakon lodi fiye da ƙima da ake yi wa motoci lamarin da ya sa za a ƙara adadin tarar da ake cin direbobin da suka saɓa doka daga Cedi 5,000 zuwa Cedi 50,000.
Gwamnatin Ghana ta bayyana cewa za ta ɗauki matakai masu tsauri kan direbobin da ke ɗaukar kaya fiye da ƙa'idar nauyin da aka ƙayyade domin kare titunan ƙasar daga lalacewa da wuri.
Ɗaya daga cikin waɗannan matakai shi ne ƙara yawan tarar da ake cin direbobin da suka saɓa doka daga Cedi 5,000 zuwa Cedi 50,000.
Ministan Tituna na Ghana Mista Kwame Governs Agbodza ne ya bayyana hakan a yayin gabatar da jawabi a wani taro a Accra babban birnin ƙasar a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa hanyoyin ƙasar da dama sun lalace sakamakon lodi fiye da ƙima da ake yi wa motoci.
Ministan ya bayar da misali da hanyar Takwa wadda ya ce ba ta wuce shekara guda da aka yi ta ba amma ta lalace saboda yadda ake yin lodin da ya wuce ƙima.
“Mun ba da shawarar a ƙara tsananta hukunci ga waɗanda ba za su bi doka ba su kuma ci gaba da lodin kaya fiye da ƙa’ida. Don haka za ku ga cewa za a ƙara kuɗaɗen tara da cajin da ake biya. Muna da niyyar ƙara tara daga Cedi 5,000 zuwa Cedi 50,000,” in ji Mista Agbodza.
Ya ƙara da cewa an kafa kwamitin ƙwararru daga sassa daban-daban domin sake dubawa da inganta tsarin da ake bi na yi wa motoci lodi.
Comments
No comments Yet
Comment