Sport
Dollar
40,7015
0.02 %Euro
47,2204
1.43 %Gram Gold
4.394,9300
2.22 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%'Yan bindigar sun kai hare-hare biyu a yankin Maradi na Jamhuriyar Nijar inda suka kashe mutum uku tare da sace matan aure da 'yan mata da wata bazawara.
Bayan samun sauƙi na tsawon makonni daga hare-hare ‘yan bindiga a yankin Maradi na Nijar, an sake fuskantar wasu munanan hare-hare biyu, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da kuma sace wasu mutane.
Hare-haren biyu sun faru ne tsakanin 29 zuwa 30 ga watan Yuli a Guidan Roumdji da Madarounfa, kamar yadda jaridar ActuNiger ta ruwaito.
Hari na farko dai an kai shi ne a ranar 29 ga Yuli da misalin ƙarfe 11 na dare a ƙauyen Garin Kelkele wanda ke ƙarƙashin gari nan na kan iyaka na Tibiri da ke Guidan Roumdji.
Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga masu ɗumbin yawa sun kutsa cikin garin inda suka sace mutum huɗu da shanu da dama.
Sai dai rahotannin sun bayyana cewa an gano wasu daga cikin shanun da aka sace, duk da cewa ba a bayyana yadda hakan ta faru ba.
Bayan awanni 24, a ranar 30 ga Yuli da misalin ƙarfe 11:30 na dare, an sake kai hari a Gandu, wani gari da ke cikin ƙaramar hukumar Sarkin Yamma a Madarounfa
Sai dai rahotannin sun ce harin da aka kai a Madarounfa ya fi na Guidan Roumji muni. ‘Yan bindigan sun kashe mutum uku duka maza sannan sun sace matan aure biyu da bazawara ɗaya da ‘yan mata huɗu.
Tuni dai jami’an tsaron Nijar tare da haɗin gwiwar mazauna yankin suka ƙaddamar da bincike domin ceto waɗanda aka sace.
Sai dai har yanzu al’ummar yankunan na ci gaba da zama cikin fargaba da firgici inda suke kira da babbar murya kan a ƙara inganta tsaro a yankunan da ke kan iyaka da kuma hanyoyin da suke bi zuwa gonaki.
Wannan sabon harin ya sake bayyana yadda wasu yankuna a Maradi ke ci gaba da kasancewa cikin matsanancin hadari, musamman bayan jerin rikice-rikicen da suka addabi yankin a 'yan shekarun nan.
Comments
No comments Yet
Comment