Dollar

40,6705

0.08 %

Euro

46,4448

-0.12 %

Gram Gold

4.315,3200

0.37 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ɓarkewar annobar kwalara a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Nijeriya ya jawo fargabar cewa za a iya samun yaɗuwar cutar a tsakanin ƙasashe maƙwabta, in ji Hukumar Majalisar Dinkin Duniya

MDD ta ce yara 80,000 na cikin haɗarin kamuwa da cutar kwalara a Yammaci da Tsakiyar Afirka

Kimanin yara 80,000 suna cikin babban haɗarin kamuwa da cutar amai da gudawa (kwalara) yayin da damina ta kankama a yankin Yammaci da Tsakiyar Afirka, in ji Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a ranar Laraba.

A cikin wata sanarwa, hukumar ta ce yaduwar cutar a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Nijeriya ya ƙara haɗarin yaɗuwar kwalarar a ƙasashe maƙwabta.

A Kongo, wacce ita ce ƙasar da cutar ta shafa a yankin, jami'an lafiya sun bayar da rahoton cewa fiye da mutum 38,000 da suka kamu da cutar, sai kuma mutum 951 da suka mutu a watan Yuli, inda yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar suka kai kaso 25.6% na waɗanda suka kamu, a cewar UNICEF.

Sauran ƙasashen da ke fama da cutar kwalara sun haɗa da Chadi da Jamhuriyar Kongo da Ghana da Ivory Coast da Togo.

‘Ya zama dole a ɗauki matakan gaggawa’

UNICEF ta bayyana cewa akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa don hana yaduwar cutar da kuma daƙile ta a fadin yankin.

“Ruwan sama mai yawa da ambaliyar ruwa da kuma yawaitar gudun hijira suna ƙara haɗarin yaduwar kwalara kuma suna sanya rayuwar yara cikin haɗari,” in ji Gilles Fagninou, daraktan UNICEF na yankin Yammaci da Tsakiyar Afirka.

“Tare da rashin samun ruwan sha mai tsabta da yanayin tsafta da ya riga ya tabarbare, ya zama dole a ɗauki matakan gaggawa. Wannan batu ne na rayuwa,” Fagninou ya ƙara da cewa.

Yara, musamman waɗanda ke ƙasa da shekaru biyar, sun fi fuskantar haɗarin kamuwa da cutar kwalara, saboda abubuwa kamar rashin tsafta da rashin wuraren wanka masu kyau da ruwan sha mai tsabta.

Don ƙara ƙarfafa ayyukan gaggawa na yakar kwalara a fadin yankin cikin watanni uku masu zuwa, UNICEF na Yammaci da Tsakiyar Afirka na buƙatar dala miliyan 20 don samar da tallafi mai muhimmanci.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#