Dollar

40,5860

-0.48 %

Euro

47,7946

-0.42 %

Gram Gold

4.353,4200

-1.37 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce wannan matakin da ta ɗauka kan Nijar zai ci gaba da kasancewa har sai ta warware matsalolin da take da su da ƙasar.

Amurka ta dakatar da ayyukan bayar da biza a ofishin jakadancinta na Nijar

Kasar Amurka ta dakatar da dukkan ayyukan bayar da biza a ofishin jakadancinta da ke Yamai, babban birnin Nijar, kamar yadda wani mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya bayyana, da kuma wata takarda da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani a ranar Asabar.

A cikin takardar, mai ɗauke da kwanan wata na 25 ga Yuli, ba a bayyana dalilin wannan mataki ba, amma mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce dakatarwar, wadda ta shafi dukkan nau’ikan biza na masu shige da fice da waɗanda za su je zama na tsawon lokaci, za ta ci gaba da kasancewa har sai Washington da shawo kan “matsalolin da take da su da gwamnatin Nijar.”

Mai magana da yawun ma’aikatar bai bayar da ƙarin bayani kan dalilin ba, amma ya ce mafi yawan nau’ukan biza na diflomasiyya da na hukumomi ba su cikin waɗanda aka dakatar.

“Gwamnatin Trump ta mayar da hankali kan kare kasarmu da ’yan kasarmu ta hanyar tabbatar da mafi girman matakan tsaro na ƙasa da kuma tsaron jama’a ta hanyar tsarin bayar da biza,” in ji mai magana da yawun ma’aikatar.

Takardar diflomasiyyar ta kuma umarci jami’an bayar da biza a wasu ofisoshin bayar da biza su yi amfani da “tsauraran matakai” wajen tantance masu neman biza ta shiga Amurka domin yawon buɗe ido ko zama na gajeren lokaci.

Amurkar ta ce a cikin masu zuwa yawon buɗe ido tana samun kaso 8 cikin 100 na masu wuce kwanakin da aka ba su na zama a Amurka sai kuma bizar ɗalibai da masu zuwa halartar aiki ko taro inda ake samun kaso 27 masu wuce adadin kwanakin da aka gindaya musu.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#