Dollar

40,4274

0.07 %

Euro

47,3913

0.08 %

Gram Gold

4.417,2600

0.13 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Gwamnatin Nijar ta ƙaddamar da bincike kan sayar da dutsen meteorite a Amurka kan kusan dala miliyan biyar wanda aka gano a yankin Agadez.

Nijar ta ƙaddamar da bincike kan dutsen meteorite da aka tsinta a ƙasarta aka sayar a Amurka

 Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ƙaddamar da bincike kan sayar da wani dutsen meteorite da aka gano a yankin Agadez, wanda aka ce an sayar da shi a kasar Amurka a kan kusan dala miliyan 5.

“Majalisar Ministoci ta samu rahoto kan sayar da wani dutsen meteorite a Amurka a kan kusan dala miliyan 5, wanda aka gano a yankin Agadez,” kamar yadda wata sanarwa da majalisar ministocin ƙasar ta fitar bayan taron ministoci. 

Majalisar ta bayyana damuwa kan wannan lamari, tana mai cewa alamu sun bayyana ƙarara na fataucin kayayyaki tsakanin ƙasa da ƙasa ba bisa ƙa’ida ba.

“Saboda haka, Majalisar Ministoci ta umarci Ministan Ma’adanai, Ministan Ilimin Gaba da Sakandare da Ministan Shari’a su gudanar da bincike don gano hakikanin gaskiyar wannan lamari,” in ji sanarwar.

A ranar Larabar da ta gabata ne, gidan sayar da kayayyaki na ƙima na Sotheby da ke birnin New York a Amurka, ya sayar da dutsen da aka gano a shekarar 2023 a Nijar, wanda aka bayyana a matsayin “dutsen meteorite mafi girma daga duniyar Mars da aka taɓa samu a doron ƙasa.”

An ce dutsen, wanda aka sanya wa suna NWA 16788, yana da nauyin kilogiram 24.5 kuma yana da tsawon 38.1 cm.

Rahotannin kafafen watsa labarai na yamma sun bayyana cewa wani “mai farautar duwatsun da suka faɗo daga sararin samaniya” ne ya gano shi, kafin a kai shi don bincike a Cibiyar Ilimin Taurari ta Shanghai a China, inda aka tabbatar da cewa dutsen na daga cikin nau'in Mars.

Haka kuma an kuma bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin nau’in “shergottines”, wani nau’i mai wuya da ke fitowa daga duniyar Mars.

Masana kimiyya sun bayyana dutsen meteorite a matsayin “tsatson duwatsu da suka rage daga asteroid ko comet da suka shiga cikin iskar doron duniya.”

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#