Sport
Dollar
40,4343
0.24 %Euro
47,1614
0.49 %Gram Gold
4.349,9900
0.54 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Jami'an Operation Niya da ke Nijar sun samu nasarori a farmaki daban-daban da suka kai, daga ciki har da kama masu haɗa bama-bamai da masu sayar wa 'yan ta'adda dabbobin sata da masu yi wa 'yan ta'adda fasa-ƙwaurin man fetur.
Jami’an tsaron Operation Niya a Nijar sun gudanar da ayyuka da dama na daƙile ta’addanci a faɗin ƙasar inda suka sanar da samun nasarori a yankunan Téra da Tamou inda suka daƙile hanyoyin jigilar makamai da sauran kayan aiki ga ‘yan ta’addan da ke yankunan.
A ranar 14 ga Yuli, a unguwar Château 2 da ke Téra, jami’an tsaro sun kama wani mutum da ake zargi da boye ɗan uwansa wanda ke fuskantar tuhuma kan laifukan ta’addanci. An ƙwato wasu muhimman kayayyaki a wajen kamen, waɗanda suka ƙara tabbatar da zargin alaka da ƙungiyar ta’addanci da ake yi wa mutumin.
Washe gari a ranar 15 ga Yuli, wani mutum marar takardun shaida ya shiga hannun jami’an tsaro a shingen bincike na Samira, bayan da ya yi yunƙurin kai hari kan sojoji yayin da suke masa tambayoyi.
Rahotannin leƙen asiri sun nuna cewa mutumin ya bar yankin Kokoloko, wanda aka sani a matsayin mafakar ‘yan ta’adda. Wannan ya sanya jami’an tsaro ƙarfafa sintiri a kudancin yankin Tamou.
A ranar 17 ga Yuli, watarundunar sintiri ta haɗin gwiwa ta cafke mutum uku da ke ɓuya a da ke kudu maso gabashin Tamou. Ɗaya daga cikinsu na ɗauke da kayan haɗa nakiya, lamarin da ya tabbatar da kasancewar wata cibiyar samar da kayan aiki ga kungiyoyin makamai. Binciken farko ya nuna cewa waɗanda aka kama na cikin wata ƙungiyar tallafa wa ‘yan ta’adda da kayan abinci da makamai.
A kasuwar dabbobi ta Téra, jami’an tsaro sun kama wani mutum da yake ƙoƙarin sayar da dabbobin da aka sace domin amfanin ƙungiyoyin ta’adda. An same shi da CFA 350,000, da ake zargin ya same su ne daga haramtaccen ciniki. Wannan na nuna yadda wasu hanyoyin kasuwanci ke taimaka wa ta’addanci kai tsaye ko a kaikaice.
A wani farmaki a hanyar Téra zuwa Yamai, jami’ai sun kama masu fasa-kwauri biyu da wani ma’aikacin matatar man fetur a kusa da matatar Morey, tare da ganga 15 na man fetur, ciki har da guda biyar da aka riga aka cika. Waɗanda ake zargin sun amsa cewa sun bai wa jami’an tsaro cin hanci domin su wuce ba tare da an tsaida su ba — abin da ke ƙara bayyana yadda fasa-ƙwaurin man fetur ke tallafa wa ayyukan kungiyoyin bindiga.
Comments
No comments Yet
Comment