Dollar

40,3906

-0.01 %

Euro

47,2592

0.43 %

Gram Gold

4.406,6200

1.29 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

An dakatar da Mista Divine Selasi Agbeti kan zargin amfani da soja a matsayin dogari musamman a wuraren da ake taro ba tare da izini ba.

Shugaba John Mahama na Ghana ya dakatar da shugaban hukumar kula da tsaron intanet ta ƙasar

Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya dakatar da Darakta Janar na Hukumar Kula da Tsaron Intanet ta Ghana, Divine Selasi Agbeti na tsawon mako biyu.

Ana zargin Agbeti da amfani da soja a matsayin dogari musamman a wuraren da ake taro ba tare da izini ba. Wannan lamari ya tayar da ƙura matuƙa inda ake ganin hakan ya saɓa wa doka da kuma barazana ga tsaron ƙasa.

A wata takarda da sakataren gwamnatin Ghana Dakta Callistus Mahama ya saka wa hannu, shugaban ƙasar ya nuna rashin jin daɗinsa kan abubuwan da Agbeti ya aikata, inda ya bayyana ɗabi’unsa a matsayin “marasa kyau kuma abin kunya ga gwamnati.”

A baya dai Ministan Tsaron Ghana Dakta Omane Boamah ya bayar da umarni inda ya gargaɗi jam’ian gwamnati kan amfani da sojoji a matsayin dogarai ba tare da samun izini ba.

Haka kuma gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa akwai yiwuwar ɗaukar ƙarin matakai idan sakamakon binciken da za a gudanar ya fito.

An naɗa Agbeti a matsayin shugaban Hukumar Kula da Tsaron Intanet na Ghana a Maris ɗin 2025, inda ya gaji Dakta Albert Antwi-Boasiako, wanda ya jagoranci hukumar tun daga 2017 bayan kafa ta.

 

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#