Sport
Dollar
40,2850
0.08 %Euro
46,8716
-0.13 %Gram Gold
4.321,3900
-0.25 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Sojojin Faransa kusan 350 za su bar ƙasar da ke Yammacin Afirka a ranar Alhamis inda Faransar za ta mika Camp Geille, wanda shi ne sansaninta mafi girma a ƙasar, tare da filin jirgin sama na Dakar.
Faransa za ta mika sansaninta na ƙarshe na soji a Senegal a ranar Alhamis, wanda hakan zai kawo ƙarshen kasancewar sansanonin sojin Faransa a yankin Yammaci da Tsakiyar Afirka.
Janyewar sojojin Faransa daga Senegal bayan shekaru 65, ta biyo bayan irin wannan janyewar a wasu ƙasashen nahiyar, inda ƙasashen da Faransar ta mulka a baya ke ta juya mata baya.
Sojojin Faransa kimanin 350 waɗanda suka rage, wadanda galibinsu ke aiki tare da sojojin Senegal, za su bar kasar ta Yammacin Afirka bayansun shafe watanni uku suna janyewa. Faransa ta fara miƙa sansanoninta ga Senegal tun watan Maris.
Bayan samun nasara a zaɓen 2024 tare da alƙawarin kawo sauyi mai girma, Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya buƙaci Faransa ta janye sojojinta daga ƙasar kafin shekarar 2025.
Sansani mafi girma
Ba kamar shugabannin wasu ƙasashen da Faransa ta mulka ba irin su Burkina Faso, Mali da Nijar, Faye ya dage cewa Senegal za ta ci gaba da aiki tare da Paris.
A wani biki da za a gudanar a Dakar, Faransa za ta mika Camp Geille, wanda shi ne sansaninta mafi girma a ƙasar, tare da filin jirgin sama na Dakar.
Ana sa ran Shugaban Hafsoshin Sojin Senegal, Janar Mbaye Cisse, da Janar Pascal Ianni, wanda ke jagorantar sojojin Faransa a Afirka, za su halarci bikin.
Tun bayan samun 'yancin kai a shekarar 1960, Senegal ta kasance ɗaya daga cikin abokan Faransa mafi aminci a Afirka, inda take karɓar baƙuncin sojojin Faransa a tsawon tarihi.
Faye, wanda ya tsaya takara da alƙawarin sauya salon mulki, ya bayyana cewa Senegal za ta rinƙa alaƙa da Faransa kamar yadda take alaƙa da sauran ƙasashen waje.
Comments
No comments Yet
Comment