Sport
Dollar
40,1901
0.22 %Euro
47,1146
0.08 %Gram Gold
4.336,9600
1.24 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Yara uku na daga cikin mutum 11 da dakarun RSF suka kashe sannan suka jikkata aƙalla 31, daga ciki har da mata tara, wasunsu na da juna biyu, kamar yadda likitoci suka tabbatar.
Aƙalla fararen hula 11, ciki har da yara uku, sun rasa rayukansu a hannun dakarun Rapid Support Forces (RSF) a Jihar Kordofan ta Arewa da ke yammacin Sudan, kamar yadda likitocin yankin suka bayyana a ranar Lahadi.
A cikin wata sanarwa, Cibiyar Likitocin Sudan ta bayyana cewa mutum 31 sun jikkata, ciki har da mata tara, wasu daga cikinsu masu juna biyu, a harin da aka kai yankin Shaq Al-Noum a jihar.
Sanarwar ta kira wannan hari da suna "ɗaya daga cikin munanan hare-haren da suka saɓa wa dukkan ƙa'idojin jin ƙai da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa."
Cibiyar ta yi kira ga al'ummar duniya, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da Ƙungiyar Tarayyar Afirka, "da su ɗauki mataki nan take kuma a tsanaki don dakatar da irin wannan take haƙƙin, tare da yin aiki don gurfanar da masu aikata laifukan a gaban shari'a."
Ƙaruwar hare-hare
Ba a samu wani bayani kai tsaye daga dakarun na RSF ɗin kan wannan sanarwa ba.
Jihar Kordofan ta Arewa ta sha fama da ƙaruwar hare-hare yayin da rikici tsakanin sojojin Sudan da RSF ke ci gaba da mamaye kasar.
Sojoji da RSF sun fara faɗa tun watan Afrilu na shekarar 2023, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da mutum 20,000 tare da raba mutum miliyan 14 da muhallansu, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin cikin gida suka bayyana.
Duk da haka, bincike daga jami'o'in Amurka ya ƙiyasta adadin waɗanda suka mutu ya kai kusan 130,000.
Comments
No comments Yet
Comment