Sport
Dollar
40,2300
0.09 %Euro
47,0485
-0.19 %Gram Gold
4.354,8900
0.46 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Tsohon shugaban ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya, kamar yadda mai magana da yawunsa Garba Shehu ya tabbatar.
Tsohon shugaban Nijeriya kuma shugaban mulkin soja a baya, Muhammadu Buhari, ya rasu yana da shekaru 82 a birnin Landan, ƙasar Birtaniya, kamar yadda iyalan marigayin suka tabbatar da rasuwarsa da yammacin Lahadi a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Malam Garba shehu ya fitar.
Buhari ya rasu ne da misalin 4:30 na yamma agogon Landan bayan fama da rashin lafiya, kamar yadda sanarwar Fadar Shugaban Nijeriya ta sanar a ranar Lahadi.
Sanarwar, wacce Bayo Onanuga, mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ya fitar, ta ce Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalen marigayin, sannan ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima ya tafi Landan domin tahowa da gawar marigayin.
Ba a bayyana takamaimen rashin lafiyar da ya yi ba, sai dai a kwanakin baya wasu rahotanni sun ce an shigar da shi dakin kula da lafiya ta musamman a wani asibiti a Landan.
Sha’anin lafiyarsa ta jima tana janyo tambayoyi musamman a lokacin da yake shugabancin ƙasa daga 2015 zuwa 2023, inda ya yi fama da doguwar jinya a ƙasashen waje.
Buhari, wanda ya kasance babban janar na soji, ya fara hawa mulki ne ta hanyar juyin mulki a watan Disamban 1983, inda ya kifar da gwamnatin farar hula ta Shugaba Shehu Shagari.
Mulkinsa ya shahara da tsauri da kuma yaƙi da rashin ɗa’a. Ya kafa shahararren shirin “Yaƙi da Rashin Da’a”, kafin daga bisani a yi masa juyin mulki a 1985 inda Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya maye gurbinsa.
Bayan komawar Nijeriyar tsarin dimokuraɗiyya a 1999, an yi ta kiraye-kiraye ga Muhammdu Buhari kan ya shiga fagen siyasa, wand a lokacin ake da fatan zai iya magance matsalolin da Nijeriya ke fama da su.
Ya shiga harkokin siyasar a shekarun 2000, inda ya yi takarar shugaban ƙasa sau uku ba tare da nasara ba, kafin daga baya ya samu nasara a 2015. Wannan nasarar tasa ta zama tarihi, domin shi ne shugaban ƙasa na farko da ya doke mai ci a zaɓe a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma ƙoƙarin murkushe 'yan Boko Haram a Arewa maso Gabas. Masoyansa sun yaba masa da tsayuwar daka wajen kare dukiyar ƙasa, sai dai masu suka sun zarge shi da fifita wasu, da tsaurin ra’ayi, da kuma gazawa wajen farfaɗo da tattalin arziki.
Bayan ya kammala wa’adinsa na biyu a watan Mayun 2023, Buhari ya koma garinsu Daura a Jihar Katsina, inda dama tun kafin ya sauka mulki ya sha nanata cewa Daura zai koma domin aikin gona da kula da dabbobinsa.
Buhari ya bar matarsa Aisha Buhari, da ‘ya’ya da jikoki.
Comments
No comments Yet
Comment