Sport
Dollar
40,1901
0.22 %Euro
47,1146
0.08 %Gram Gold
4.336,9600
1.24 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Janar Oluyede ya yi wannan kira ne a Abuja a wajen Taron Ƙasa kan Abinci, da Abinci Mai Gina Jiki da kuma Tsaron Abinci, wanda kwamitin Majalisar Wakilai kan Tsaron Abinci na Ƙasa ya shirya.
Babban Hafsan rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya Laftanal Janar Olufemi Oluyede, ya nemi Majalisar Dokokin kasar da ta ɗabbaka wata doka da za ta haramta kiwon sake da samar da hanyoyin killace dabbobi da makiyaya za su dinga amfani da su.
Janar Oluyede ya yi wannan kira ne a Abuja a wajen Taron Ƙasa kan Abinci, da Abinci Mai Gina Jiki da kuma Tsaron Abinci, wanda kwamitin Majalisar Wakilai kan Tsaron Abinci na Ƙasa ya shirya.
Babban Hafsan Sojin ya jaddada buƙatar gaggawa ta rungumar tsarin burtalai a matsayin wata manufa ta ƙasa da za ta taimaka wajen warware matsalar da ke kawo tarnaƙi ga bunƙasar samar da abinci a Nijeriya, yana mai cewa yin kiwo a barkatai a yanzu ba abin da zai ɗore ba ne.
A cewar babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya, rundunar sojin ƙsar ta kafa matakai daban-daban da nufin dakile rikicin manoma da makiyaya.
Rear Admiral Yusuf Sani Idris, wanda ya wakilci babban hafsan hafsoshin ruwa a taron, shi ma ya bayyana irin gudunmawar da sojojin ruwa suka bayar ta hanyar kafa Admiralty Farms Limited, tare da gonakin da ke aiki a kusan dukkanin shiyyoyin ƙasar shida.
Ya bayyana cewa, gonakin na samar da wadataccen abinci da mai gina jiki ga manoma, yayin da ake shirin fadada ta zuwa wasu shiyyoyi.
Mataimakin kwamanda-janar Besong Ogar, wanda ya wakilci kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya ta Nijeriya (NSCDC), ya jaddada bukatar yin musayar bayanai kan lokaci domin magance tabarbarewar tsaro da ke shafar gonaki.
A nasa bangaren, Dakta Chike Okafor, shugaban kwamitin majalisar mai kula da harkokin abinci, ya jaddada kudirin kwamitin na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya, ya kara da cewa zaman lafiya da tsaro na da matukar muhimmanci ga manoma da hukumomin tsaro baki daya.
Comments
No comments Yet
Comment