Sport
Dollar
40,1729
0.22 %Euro
47,0757
0.06 %Gram Gold
4.336,2100
1.22 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A baya-bayan nan ne ce-ce-ku-ce mai zafi ya ɓarke a jihar Kano, bayan da wani sanannen malamin Mususlunci, Sheikh Lawan Triumph ya gabatar da karatu kan wani hadisi da wasu ke dangantawa da rashin girmamawa ga Manzon Allah SAW.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano a Nijeriya ta yi kira da a kwantar da hankula a jihar tare da kiyaye doka, bayan dambarwar da ta taso kan wa’azin wani malami mai suna Sheikh Lawan Triumph.
A baya-bayan nan ne ce-ce-ku-ce mai zafi ya ɓarke a jihar, tun bayan da Sheikh Triumph ya gabatar da karatu a kan wani hadisi da wasu ke dangantawa da rashin girmamawa ga Manzon Allah SAW.
A sanarwar da rundunar ta wallafa a shafin mai magana da yawunta a Facebook, Abdullahi Kiyawa a ranar Juma’a, ta ce “A yayin da muke tabbatar da cewa kowa yana da damar gudanar da addininsa, muna kuma taka-tsantsan kan buƙatar tabbatar da zaman lafiya.
“A martaninmu kan lamarin na ranar 10 ga watan Yulin 2025, Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kano ya gayyaci malamin, inda aka gudanar da tattaunawa ta masu ruwa-da-tsaki da suka haɗa da jami’an gwamnati, da malamai da wakilan al’umma don warware damuwar da aka gabatar, da tabbatar da cewa an ɗauki dukkan matakan da suka kamata don hana ɓarkewar rigima,” in ji sanarwar.
Daga nan sai rundunar ‘yan sandan ta nemi dukkan al’umma da su kwantar da hankulansu, tare da kauce wa duk wani abu da zai iya ta’azzara yanayin.
“Yana da kyau a dinga girmama haƙƙoƙi da abin da mutane suka yi imani da shi, da kuma bin doka da oda waɗanda su ke tafiyar da al’ummarmu, a ƙoƙarinmu na samar da ‘yancin ibada da sauransu.
‘Yan sandan sun kuma ce suna so daga yanzu duk wanda yake da wani ƙorafi ko hujja to ya mika su ga hukumomin da suka dace, maimakon yin abubuwan da za su iya haifar da cin zarafi ko maganganu masu tayar da hankali a shafukan sada zumunta.
“Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta dukufa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar tare da kiyaye ka’idojin adalci, da mutunta duk wani dan kasa ba tare da la’akari da asalinsa ko nasabarsa ba.
Muna kira ga jama'a da su ba mu hadin-kai wajen inganta yanayin zaman lafiya da jituwa tare da yin aiki tare don gina al'umma mai hadin-kai,” kamar yadda sanarwar ta faɗa.
Comments
No comments Yet
Comment