Sport
Dollar
40,1769
0.23 %Euro
47,0553
0.04 %Gram Gold
4.330,6100
1.09 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Tuggar ya ce ba za su taɓa bayar da kai bori ya hau ba game da kudirin gwamnatin Amurka na aika musu 'yan ƙasar Venezuela da ke Amurka da ake shirin kora, daga ciki har da fursunoni.
Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya ba za ta amince da matsin lamba daga gwamnatin Donald Trump ba wajen karɓar ‘yan Venezuela da Amurka ke shirin korowa.
Tuggar ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin ɗin Channels a Nijeriya a ranar Alhamis, inda ya ce Nijeriya tana da nata matsalolin kuma ba za ta zama wurin zubar da fursunonin Venezuela daga Amurka ba a lokacin da Trump ke ci gaba da matsa wa ‘yan gudun hijira marasa takardu.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya halarci taron BRICS tare da sauran shugabannin duniya a birnin Rio de Janeiro na Brazil daga 6 zuwa 7 ga Yulin, 2025.
A ranar ƙarshe ta taron ƙungiyar BRICS mai mambobi 11 wadda ƙasar China ke da ruwa da tsaki sosai a ciki, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da ƙarin harajin kashi 10 cikin 100 kan kasuwancin kasashen BRICS da suka haɗa da China, India da Nijeriya, waɗanda ya kira "kasashen da ke adawa da Amurka."
Tuggar ya ƙara da cewa ba lallai ƙarin harajin ya danganci alaƙar Nijeriya da ƙasashen BRICS ba.
“Ya kamata ku fahimci cewa Amurka tana matsa wa kasashen Afirka lamba sosai domin su karɓi 'yan Venezuela da za a kora daga Amurka, wasu ma kai tsaye daga gidajen yari.
“Zai yi wuya ƙasashe irin Nijeriya su karɓi fursunonin Venezuela a Nijeriya. Muna da isassun matsalolinmu; ba za mu iya karɓar 'yan Venezuela da aka kora zuwa Najeriya ba. Tuni muna da mutane miliyan 230,” kamar yadda Tuggar ya ƙara da cewa.
Comments
No comments Yet
Comment