Sport
Dollar
40,1901
0.22 %Euro
47,1146
0.08 %Gram Gold
4.336,9600
1.24 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Kotun ta yanke hukuncin ɗauri na shekara 10 har zuwa 30 ga mutanen da aka samu da laifin alaƙa da Boko Haram a shari'ar da ake gudanarwa a Kainji da ke Jihar Neja.
Nijeriya ta yanke hukunci ga mutum 44 da aka samu da laifin tallafa wa ayyukan ta'addanci, inda aka yanke musu hukunci na zaman gidan yari har zuwa na shekara 30, in ji kakakin wata hukumar yaki da ta'addanci a ranar Asabar.
Waɗanda aka yanke wa hukuncin suna cikin mutane 54 da aka gurfanar a gaban kotuna hudu na musamman da aka kafa a sansanin soja da ke garin Kainji, a tsakiyar jihar Neja, kamar yadda Abu Michael, kakakin cibiyar yaki da ta'addanci ta Nijeriya ya bayyana a wata sanarwa. Ya ce an dage sauraron shari'ar sauran mutane 10 zuwa wani lokaci nan gaba.
A ranar Laraba ne Nijeriya ta ci gaba da shari'ar waɗanda ake zargi bayan shekaru bakwai bayan ta dakatar da shari’ar fiye da mutum 1,000 da ake zargi da alaƙa da ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram, wacce ta fara ayyukan ta’addanci tun daga shekarar 2009.
"Hukuncin da aka yanke a shari'ar ya kai ga aiwatar da ɗaurin shekara 10 zuwa 30, inda dukansu za a aiwatar da su da horo mai tsanani,” in ji Michael.
"Da wannan hukunci na baya-bayan nan, Nijeriya ta samu nasarar kammala shari'o'i 785 da suka shafi tallafa wa ayyukan ta'addanci da sauran laifukan da suka shafi ta'addanci," in ji sanarwar.
Bazuwar ayyukan Boko Haram
Tashin hankalin Boko Haram, wanda ya fara a arewa maso gabashin Nijeriya, ya bazu zuwa maƙwabtan ƙasashe irin su Kamaru, Chadi da Nijar, inda ya kashe dubban mutane tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu.
A watan Oktoban 2017, Nijeriya ta fara shari'ar waɗanda ake zargi da ta'addanci, fiye da shekaru takwas bayan fara tashin hankalin.
Dubban 'yan Boko Haram da iyalansu sun mika wuya tsawon shekaru yayin da sojoji suka ƙara ƙaimi a ayyukansu.
Wannan matakin shari'ar, wanda ya ɗauki tsawon watanni biyar, ya kai ga yanke hukunci ga mambobi 200 na ƙungiyar Boko Haram, inda aka yanke musu hukunci daga "hukuncin kisa da ɗaurin rai da rai zuwa ɗaurin shekaru 20 zuwa 70," in ji Michael.
Laifukan da aka yanke musu hukunci sun haɗa da hare-hare kan mata da yara, lalata wuraren ibada, kashe fararen hula, da sace mata da yara.
Comments
No comments Yet
Comment