Sport
Dollar
40,1901
0.22 %Euro
47,1146
0.08 %Gram Gold
4.336,9600
1.24 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Oxfam ta ce cewa manufofin gwamnati sun fi takura wa talakawa kuma ta zargi "tsauraran" manufofin Asusun Ba da Lamuni na Duniya da ƙara janyo rashin daidaito.
'Yan Afirka hudu mafi arziki sun fi kusan rabin al'ummar nahiyar miliyan 750 arziki, in ji kungiyar yaƙi da talauci ta Oxfam, a wani rahoto da ta wallafa a ranar Alhamis, tana mai gargadin cewa ƙaruwar rashin daidaito na kawo cikas ga dimokradiyya.
Sai dai sunan attajirin nan ɗan Nijeriya, Aliko Dangote kawai Oxfam ɗin ta ambata a rahoton nata.
Amma bisa ga rahoton Forbes, sauran uku cikin hudu mafi arziki sun hada da Johann Rupert da Nicky Oppenheimer daga Afirka ta Kudu, da kuma ɗan kasuwar Masar, Nassef Sawiris.
A cikin shekaru biyar da suka gabata, attajiran Afirka sun ga ƙaruwar arzikinsu da kashi 56 cikin 100, inda mafi arziki a cikinsu suka samu ƙarin riba mai yawa, in ji Oxfam.
Rahoton ya kuma nuna cewa kusan rabin kasashe 50 da suka fi fuskantar rashin daidaito a duniya a nahiyar Afirka suke.
Oxfam ta zargi manufofin gwamnati da cewa suna fifita masu arziki fiye da talakawa, suna ba da damar attajirai su ƙara tara dukiya.
"Yawancin kasashen Afirka ba sa amfani da tsarin haraji mai ci gaba don karbar haraji daga masu arziki sosai da kuma rage rashin daidaito," in ji rahoton.
Haka kuma, rahoton ya zargi manufofin Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da cewa suna kara rashin daidaito, tare da zargin kwararar kudade ta hanyar da ba ta dace ba - musamman amfani da wuraren ɓoye haraji don ɓoye dukiya a kasashen waje.
Kungiyar ta ce rashin daidaito na kawo cikas ga dimokuradiyya, yana hana rage talauci kuma yana ƙara tabarbarewar yanayi, tare da cewa "riƙon iko na masu arziki yana lalata manufofin gwamnati masu amfani ga talakawa da kuma tasirin hukumomin gwamnati."
Oxfam ta ba da shawarar sake fasalin tsarin haraji a nahiyar Afirka.
A halin yanzu nahiyar tana asarar kimanin dala biliyan 88.6 a kowace shekara ta hanyar kwararar kudade ta hanyar da ba ta dace ba.
Binciken tsarin haraji na kasashe 151 ya gano cewa "Afirka ita ce kadai yankin da kasashe ba su kara yawan haraji mai tasiri tun daga shekarar 1980 ba," in ji kungiyar.
Comments
No comments Yet
Comment