Dollar

39,1011

0.04 %

Euro

44,4609

0.52 %

Gram Gold

4.202,2600

1.92 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ministan Lafiya na Sudan, Haitham Mohamed Ibrahim ya ce ana samun aƙalla mutum 600 zuwa 700 da ke kamuwa da cutar ta kwalara a kowane mako tun daga watan da ya gabata.

Ɗaruruwan mutane sun kamu da cutar kwalara a Sudan

Ma’aikatar Lafiya ta Sudan a ranar Asabar ta sanar da cewa an samu ɗaruruwan mutane da suka kamu da cutar kwalara a Jihar Khartoum cikin makonni huɗu da suka gabata.

Ministan Lafiya na Sudan, Haitham Mohamed Ibrahim a wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa ana samun aƙalla mutum 600 zuwa 700 da ke kamuwa da cutar ta kwalara a kowane mako tun daga watan da ya gabata.

Ya bayyana cewa ƙaruwar masu kamuwa da cutar ba abin mamaki ba ne, musamman bayan 'yantar da Jihar Khartoum da dawowar mazauna daga yankunan Jabal Awliya da Al Salha, wanda ya haifar da taɓarɓarewar yanayin muhalli da matsalar samun ruwan sha mai tsafta a waɗannan wurare.

A ranar Talata, sojojin Sudan sun sanar da kammala 'tsabtace' Jihar Khartoum daga dakarun Rapid Support Forces (RSF), bayan sun ƙwace yankin Al Salha, wanda shi ne sansanin ƙarshe na RSF a Omdurman da ke yammacin Khartoum.

Shirin Rigakafi

Ministan Sudan ya bayyana cewa Ofishin Gaggawa na Kiwon Lafiya na Tarayya yana aiki dare da rana don sa ido kan yanayin lafiya a yankin tare da ɗaukar matakan da suka dace don daƙile yaɗuwar cutar.

Ya ƙara da cewa ana sa ran yawan masu kamuwa da cutar zai ragu cikin makonni masu zuwa, musamman bayan fara shirin rigakafin kwalara a cikin kwanaki masu zuwa.

A ranar Juma’ar da ta gabata, ƙungiyar likitocin Sudan ta yi kira na gaggawa don magance matsalolin kiwon lafiya da ake fama da su waɗanda ɓarkewar cutar kwalara a Khartoum ta haifar. A ranar Alhamis kadai, mutum tara sun mutu yayin da aka kai sabbin mutum 521 masu fama da cutar zuwa Asibitin Koyarwa na Al-Naw da ke Omdurman.

A cewar alƙaluman hukuma na karshe da aka fitar a ranar 6 ga Mayu, adadin waɗanda suka kamu da cutar kwalara a Sudan ya kai 60,993, yayin da mutum 1,632 suka mutu.

Annobar Kasa

A ranar 12 ga Agusta, hukumomin Sudan sun ayyana cutar kwalara a matsayin annobar kasa.

A halin yanzu, sojojin Sudan sun sake karbe iko da mafi yawan yankunan Jihar Khartoum, waɗanda suka haɗa da biranen uku na babban birnin ƙasar—Khartoum, Bahri, da Omdurman—tare da yankin Gabashin Nilu.

A cikin sauran jihohi 17 na Sudan, RSF yanzu suna rike da wasu sassa na Kordofan ta Arewa da Yamma da kuma wasu wurare a Kordofan ta Kudu da jihohin Blue Nile, tare da jihohi hudu daga cikin biyar na yankin Darfur.

Tun daga watan Afrilun 2023, RSF ke gwabza faɗa da sojojin Sudan don karɓe iko da ƙasar, lamarin da ya haifar da mutuwar dubban mutane da kuma ɗaya daga cikin manyan matsalolin jin kai a duniya.

Fiye da mutum 20,000 sun mutu yayin da aka raba mutum miliyan 15 da muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin cikin gida. Binciken masana daga Amurka, duk da haka, ya nuna cewa adadin waɗanda suka mutu ya kai kimanin 130,000.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#