Sport
Dollar
40,3760
0.14 %Euro
46,9031
0.06 %Gram Gold
4.326,7100
0 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Tsohon ɗan wasan Manchester United, Ashley Young zai koma ƙungiyar da ya fara wasa, Watford, duk da ya cika shekara 40 a watan nan na Yuli.
Ƙungiyar Watford mai buga wasa a gasa mai daraja ta biyu, Championship a Ingila ta yi wa tsohon ɗan wasanta, Ashley Young tayin komawa can.
Ashley Young, wanda tsohon ɗan baya ne da ya yi suna sanda yana Manchester United ya cika shekara 40 ranar 9 ga watan Yulin 2025.
Ya buga wasa tun yana matashi a Watford, kuma ana tunanin yana da burin kammala rayuwarsa ta ƙwallo ne a can ɗin.
Ban da Man United, Young ya buga wa ƙungiyoyin Aston Villa da Inter Milan ta Italiya. Kuma a yanzu ba shi da kulob bayan ya baro Everton a ƙarshen kakar bana.
Sanda yana ganiyarsa, ya buga wa tawagar ƙasar Ingila, duk da cewa shi ɗan tsatson Jamaica ne kuma yana da katin ɗan ƙasar.
Wajen ritaya
Ko da ake mamakin me ya sa Watford za ta ɗauko ɗan wasan da ke ƙarshen tagomashin ƙwallo, Watford ta ce ba ta damu da shekaru ko kuzarinsa ba.
Ashley Young ya buga wa Everton wasanni 70 cikin shekara biyu, kuma a bara ya zama ɗan wasa na huɗu mafi tsufa da ya ci ƙwallo a gasar Firimiya.
Ita dai Watford ta ƙare kakar bana a mataki na finished 14 a gasar Championship, kuma suna fatan amfani da ƙwarewar Young don cika burinsu na kai wa gasar Firimiya.
Bayan fara buga ƙwallo ajin ƙwararru a Wartford, Ashley Young ya buga jimillar wasanni 100 cikin shekara huɗu.
Comments
No comments Yet
Comment