Sport
Dollar
39,1011
0.04 %Euro
44,4609
0.52 %Gram Gold
4.202,2600
1.92 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Salah ya zura kwallaye 28 tare da bayar da taimako 18 don jagorantar kungiyar ta Anfield taka matakin nasara, inda ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Arne Slot ta zama zakara a gasar duk da saura wasanni huɗu a kammala gasar.
An sanar da Mohamed Salah a matsayin gwarzon ɗan wasan Gasar Firimiya na bana a ranar Asabar, bayan da ɗan wasan Masar ɗin ya nuna bajinta a kakar wasa ta bana musamman bayan Liverpool ta lashe gasar ta Firimiya a karo na biyu.
Salah ya zura kwallaye 28 tare da bayar da taimako 18 don jagorantar kungiyar ta Anfield taka matakin nasara, inda ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Arne Slot ta zama zakara a gasar duk da saura wasanni huɗu a kammala gasar.
Bayan samun wannan lambar yabo a kakar 2017-18, Salah ya zama ɗan wasa na biyar a tarihi da ya lashe gasar sau biyu, bayan Thierry Henry, Cristiano Ronaldo, Nemanja Vidic da Kevin De Bruyne.
Dan wasan Masar ɗin mai shekara 32 yana kan hanyar lashe wani takalmin zinaren a matsayinsa na wanda ya fi zura ƙwallaye a kakar ta bana inda ya wuce ɗan wasan Newcastle Alexander Isak da ƙwallaye biyar kafin ranar ƙarshe ta kakar wasa a ranar Lahadi.
Kafa tarihi
Babu ɗan wasan da ya taɓa ci da ba da tallafin jimillar ƙwallaye 46 a salon gasa mai wasanni 38 a kaka guda. A wasan Liverpool da Crystal Palace na gobe Lahadi, idan Salah ya ci ƙwallo ko ya ba da tallafi, zai iya cim ma tarihin ƙwallaye 47 da Alan Shearer da Andrew Cole suka kafa tun a zamanin gasa mai wasanni 42.
Sakamakon ya wuce ko wane ɗan wasa wurin bayar da taimakon cin ƙwallaye da taimako shida, akwai yiwuwar Salah ya zama ɗan wasa na farko a tarihi da zai lashe takalmin zinare, da kyautar Golden Playmaker da kuma lambar yabo ta ɗan wasan kaka.
Salah ya kuma lashe lambar yabo ta ɗan wasan maza na shekara na Ƙungiyar ‘Yan Jarida Marubuta Wasannin Kwallon Ƙafa a karo na uku a farkon wannan watan.
Comments
No comments Yet
Comment