Sport
Dollar
40,3684
0.11 %Euro
47,0287
0.24 %Gram Gold
4.335,7700
0.21 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Baya ga Arsenal da Bayern Munich, Liverpool ta shirya tattaunawa da Real Madrid don ɗauko Rodrygo da aka sa wa farashin euro miliyan €100.
Liverpool ta shiga takara da takwararta ta Ingila, Arsenal domin neman ɗauko ɗan wasan gaban Real Madrid, Rodrygo wanda aka sa wa farashin euro miliyan €100.
Tuni Liverpool ta shirya tattaunawa da wakilan ɗan wasan ɗan asalin Brazil, wanda tun da fari aka bayyana cewa yana shirin barin Madrid sakamakon rashin samun gurbi ƙarƙashin sabon koci Xabi Alonso.
Liverpool dai na neman sabon ɗan wasan gaba don ƙarfafa tawagarta bayan lashe kofin Firimiya a Ingila na kakar 2025-26.
Sai dai kafin Liverpool ta shiga zawarcin Rodrygo a kasuwar cinikin ‘yan wasa ta bazarar nan, Arsenal da Bayern Munich suna cikin masu neman ɗauko tauraron.
Batun farashi
Amma baya ga Rodrygo, akwai wasu taurarin da Liverpool ke fatan ɗaukowa, irinsu Alexander Isak daga Newcastle da Hugo Ekitike daga PSG ta Faransa.
Ko a makon nan ma, an fara raɗe-raɗin Liverpool na son kawo Marcus Rashford daga Manchester United.
Sai dai a halin da ake ciki, farashin da Real Madrid ta gindaya wa Rodrygo ya kai euro miliyan €100 (wato dala miliyan $106), wanda masu sharhi kan wasanni ke ganin ya yi tsada sosai.
Comments
No comments Yet
Comment