Dollar

40,3616

0.13 %

Euro

47,0404

0.28 %

Gram Gold

4.329,3900

0.06 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Bayan PSG ta lallasa Real Madrid a wasan dab da na ƙarshe na gasar kulob-kulob na duniya, FIFA Club World Cup 2025, kuma yanzu za su haɗu da Chelsea don neman ɗaga kofi.

Chelsea da PSG za su yi karawar lashe dala miliyan 40 na Gasar FIFA Club World Cup

Paris Saint-Germain (PSG) ta fito fainal na Gasar FIFA ta kulob-kulob ɗin duniya da ke gudana a Amurka, bayan ta lallasa Real Madrid da ci 4-0 a daren Laraba, 9 ga Yuli.

Wannan na nufin ƙungiyar ta Faransa za ta kece raini da Chelsea ta Ingila a wasan ƙarshe na kofin da za a buga ranar 13 ga Yuli a filin wasa na MetLife da ke birnin New York.

Fabian Ruiz na PSG ne ya zura ƙwallaye biyu, yayin da Ousmane Dembele ya ci ƙwallo ɗaya tare da tallafin wata ƙwallon. Sannan Goncalo Ramos ya ci ta huɗun a minti na 87.

Golan PSG Gianluigi Donnarumma ya nuna bajinta wajen hana taurarin Madrid irin su Kylian Mbappe zura ko da ƙwallo guda.

Wannan dai shi ne karo na farko da Mbappe ya kara da tsohuwar ƙungiyarsa ta PSG, wadda ya ciyo wa ƙwallaye 256 cikin shekaru bakwai kafin ya koma Real Madrid a bara.

Kyautar dala miliyan 40

Paris Saint-Germain za ta kara da Chelsea don neman lashe zunzurutun kyautar kuɗi har dala miliyan 40 ga wanda ya yi nasara.

Ƙungiyar da ta zo ta biyu za ta samu dala miliyan $30, tare da sauran kuɗaɗen da suka samu tun a farkon shiga gasar bisa la’akari da nasarorin da suka samu zuwa yanzu.

Chelsea ce ta lashe kofin a shekarar 2021, yayin da PSG za ta yi ƙoƙarin zama ƙungiyar farko daga Faransa da za ta ɗauki kofin.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#