Dollar

40,4036

0.11 %

Euro

47,0271

0.24 %

Gram Gold

4.335,0800

0.19 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

A jawabin da ya gabatar yayin zaman, Shugaba Tinubu ya yi magana a kan ayyukan Buhari tun daga kan hidimarsa a rundunar sojin Nijeriya har zuwa zamansa Shugaban Ƙasa na farar-hula.

Abubuwan da suka faru a Taron Majalisar Zartarwa na Kasa na musamman don karrama Muhammadu Buhari

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci Taron Majalisar Zartarwa na Kasa na musamman da aka yi a fadar gwamnati a Abuja a ranar Alhamis domin karrama tsohon Shuaban Ƙasar, marigayi Muhammadu Buhari.

Taron, wanda ya samu halartar wasu daga cikin ‘ya’yan marigayin, da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, da Sakataren Gwamnati da ministocin gwamnatin Tinubu da sauran manyan jami’an gwamnati, ya mayar da hankali ne wajen tunawa da halaye da ayyukan ƙwarai na tsohon Shugaban Ƙasar.

A jawabin da ya gabatar yayin zaman, Shugaba Tinubu ya yi magana a kan ayyukan Buhari tun daga kan hidimarsa a rundunar sojin Nijeriya har zuwa zamansa Shugaban Ƙasa na farar-hula.

Ya bayyana shi a matsayin mai girmama duk wanda mu’amala ta haɗa su, ciki har da waɗanda suke ƙarƙashinsa ba tare da raini ko ƙasƙanci ba.

“Ko a lokacin mutuwa, ya nuna juriya kamar yadda ya yi a raye, babu ƙorafi ko gurnani, sai dai sadaukar da kai ga Allah. Irin wannan mutumin ne Nijeriya ta rasa. Wannan mutumin ne ƙasa ke alhinin rashinsa,” in ji Tinubu.

Waɗansu halayen Buhari da Tinubu ya sake faɗa su ne; bai yarda giyar mulki ta kwashe shi ba, mai tsayuw atsayin  daka kan duk abin da ya saka a gaba, mai kishin ƙasa da magana ɗaya.

Sannan ya yabi yadda marigayin ya koma Daura bayan da ya gama mulki, kuma bai dinga katsalandan a cikin mulkin wanda ya gaje shi ba don bai wa wasu damar ciyar da ƙasar gaba.

Bayan wannan yabo, sai kuma aka gabatar da addu’o;i ga marigayi Buhari a wajen taron.

Sai kuma Shugaban Ƙasar ya sanar da sauya sunan Jami;ar Maiduguri zuwa sunan marigayin, wato Muhammadu Buhari University,

"Kafin mu fara addu'o'i don tunawa da kuma karrama Buhari, a wannan taro na musamman – bari mu sanar da sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa Jami’ar Muhammadu Buhari," a cewar Tinubu.

A ƙarshe, an bai wa ɗan marigayin, Yusuf Buhari dama inda ya yi jawabin godiya ga gwamnatin Nijeriya, musamman ma Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, kan irin karramawar da aka yi wa mahaifinsu tun daga rasuwarsa har bayan binne shi.

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#