Dollar

39,0274

0.26 %

Euro

44,0645

-0.07 %

Gram Gold

4.121,7700

-0.51 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Dattijon ɗan wasan tsakiya na Real Madrid zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar bana, bayan shafe shekaru 13 yana taka mata leda.

Luka Modric ya aike da sakon bankwana ga masoya Real Marid

Gwarzo kuma dattijon ɗan wasan tsakiya a ƙungiyar Real Madrid ta Sifaniya, Luka Modric ya sanar da da cewa zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar bana, bayan shafe shekaru 13 yana taka leda.

Ɗan wasan ya aike da saƙon bankwana ga masoya Madrid, inda yake ambata cewa wannan wani ‘lokaci ne da ban so zuwansa ba’.

Madrid ta tabbatar da tafiyar tauraron nata wanda shekarunsa 39 a duniya, bayan da ya buga mata wasanni 590, ya kuma ci ƙwallaye 43.

Modrid ya wallafa saƙon rabuwa a shafinsa na Instagram yana bayyana cewa zai ci gaba da zama masoyin Real Madrid "tsawon rayuwarsa”.

Ya fara da cewa, "Barka masoya Real Madrid: Lokacin ya zo. Lokacin da ban so zuwansa ba, amma haka ƙwallo take, kuma a rayuwa komai yana da farko da ƙarshe...”

“Ranar Lahadi zan buga wasana na ƙarshe a [gida] Santiago Bernabéu. Na zo a 2012 cike da fatan saka rigar ƙungiya mafi girma a duniya, da kuma burin nuna bajinta”.

Ƙarewar kwantiragi

Ɗan wasan ya kammala da cewa buga wasa a Real Madrid ya sauya rayuwarsa a matsayinsa na ɗan ƙwallo, da kuma a matsayinsa na mutum.

Daga nan ya miƙa saƙon godiya ga ƙungiyar musamman ga shugabanta Florentino Pérez, da kuma abokan wasansa, da koci da ma duka waɗanda suka taimaka masa yayin zamansa a can.

Luka Modric ɗan asalin Crotia ne, ya ci kofuna har 28a Madrid, ciki har da kofin Zakarun Turai 6, da Kofin Ƙungiyoyi na Duniya 6, da LaLiga 4, da Copa del Rey 2.

A shekarar 2018, Luka Modric ya lashe kyautar Ballon d'Or, wanda ke nufin cika burikansa da samun gamsuwa da nasarorin da ya cim ma.

Tuntuni da ma rahotanni ke cewa Real Madrid ba za ta tsawaita kwantiragin Modric ba. Amma zai buga musu gasar Club World Cup a bazarar nan a Amurka.

A baya, Modric dai ya buga wa Tottenham ta Ingila, kuma yana cikin ‘yan wasa 5 kacal da suka taɓa lashe kofunan Turai har 6. Shi ne kuma ɗan wasan Real Madrid da ya fi kowa lashe kofuna a tarihin ƙungiyar.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#