Dollar

40,2292

0.13 %

Euro

46,7953

-0.2 %

Gram Gold

4.328,0800

0.21 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Harin da dakarun RSF suka kai "bashi da wata manfa ta soji" a Arewacin Kordofan, a cewar masu fafutuka.

Dakarun RSF ‘sun kashe fararen-hula kimanin 300’ a yankin da suke da karfi

Masu fafutukar kare haƙƙin bila'adam a Sudan ranar Litinin sun yi zargin cewa dakarun rundunar Rapid Support Forces (RSF) sun kashe mutane kimanin 300 a harin da suka kai a wasu ƙauyuka na Jihar Arewacin Kordofan a ranar Asabar.

Rundunar RSF ta daɗe tana fafatawa da dakarun rundunar sojin Sudan a yankin, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan fagagen daga tun da suka ƙaddamar da yaƙi da juna a watan Afrilun 2023.

Rundunar sojin Sudan ta karɓe iko na tsakiya da gabashin ƙasar, yayin da ita kuma rundunar RSF take aiki tuƙuru domin ƙarfafa ikonta a yammacin ƙasar, ciki har da Arewacin Kordofan.

Ƙungiyoyin lauyoyi masu fafutukar kare hakkin ɗan'adam a wata sanarwa da suka fitar ranar Litinin sun ce dakarun RSF sun kai hari ranar Asabar a ƙauyuka da dama da ke yankin birnin Bara, wanda ke ƙarƙashin ikonsu.

Sace kayayyaki

A wani ƙauye mai suna Shag Alnom, dakarun RSF sun kashe fiye da mutum 200 ta hanyar harbe-harbe da cinna musu wuta. Kazalika sun kai samame wasu ƙauyukan inda suka kashe fararen-hula aƙalla 38, yayin da gommai suka ɓata sannan sun kashe kayayyaki.

Washegari, dakarun RSF sun kai hari a ƙauyen Hilat Hamid inda suka kashe mutum 46, cikinsu har da mata masu juna biyu da ƙananan yara.

An tilasta wa mutum fiye da 3,400 tserewa daga yankin, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

"Mun tabbatar da cewa an kai waɗannan hare-hare ne da gangan, domin kawai mugunta da aikata laifukan yaƙi tare da keta dokokin jinƙai na ƙasashen duniya," a cewar ƙungiyar Emergency Lawyers, inda ta ɗora alhakin lamarin kan dakarun RSF.

Rashin jinƙai

Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam sun zargi RSF da aikata laifukan yaƙi, da laifuka kan bil'adama da kuma kisan ƙare-dangi.

Yaƙin basasar da ake yi a Sudan ya haifar da matsalar rashin jinƙai mafi girma a duniya, inda ya jefa fiye da rabin 'yan ƙasar cikin bala'in yunwa da cututtuka irinsu kwalara.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#