Sport
Dollar
40,5860
-0.48 %Euro
47,7946
-0.42 %Gram Gold
4.353,4200
-1.37 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci a yi gaggawar ƙara tallafin kuɗi domin farfaɗo da yankunan da rikici ya ɗaiɗaita a Sudan, a daidai lokacin da 'yan ƙasar da rikici ya raba da muhallansu suka fara komawa gida.
Fiye da mutum miliyan 1.3 da suka yi hijira daga Sudan saboda rikici sun fara dawowa gida, in ji Majalisar Dinkin Duniya inda take roƙon ƙarin tallafin ƙasa da ƙasa don taimakawa masu dawowa su sake gina rayuwarsu da aka lalata.
Fiye da mutum miliyan ɗaya da aka tilasta musu barin gidajensu sun koma gidajensu a watannin baya-bayan nan, in ji hukumomin Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma’a.
Har ila yau, 'yan gudun hijira 320,000 sun koma Sudan a wannan shekarar, galibi daga ƙasashen makwabta kamar Masar da Sudan ta Kudu.
Duk da cewa rikicin ya ragu a wasu wuraren da ake ganin suna da "ɗan tsaro," inda mutane suka fara dawowa, Majalisar Dinkin Duniya ta ce halin da ake ciki har yanzu yana da matuƙar haɗari.
Tun daga watan Afrilun 2023, Sudan ta shiga cikin rikicin neman shugabanci tsakanin shugaban sojoji Abdel Fattah al Burhan da Mohamed Hamdan Daglo, kwamandan dakarun RSF (Rapid Support Forces). Wannan ya haifar da mutuwar dubban mutane.
RSF ta rasa iko da babban birnin ƙasar, Khartoum, a watan Maris, kuma sojojin ƙasar yanzu suna da iko da tsakiya, arewaci da gabashin Sudan.
A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa, hukumar kula da masu yin ƙaura ta IOM da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNHCR, da hukumar ci gaba ta UNDP sun yi kira da a ƙara tallafin kuɗi cikin gaggawa don biyan buƙatun sake farfaɗo da rayuwar mutane yayin da suke dawowa, tare da bayyana cewa ba a ware isassun kuɗi wurin ayyukan jin ƙai.
Sudan tana da mutum miliyan 10 da aka tilasta musu barin gidajensu, ciki har da miliyan 7.7 da rikicin yanzu ya tilasta musu, in ji su. Fiye da mutum miliyan huɗu sun nemi mafaka a ƙasashen makwabta.
'Mafarki mai ban tsoro'
Sudan ita ce "ƙasa da ta fi buƙatar jin ƙai a duniya kuma wadda aka fi mantawa da ita," in ji daraktan yankin IOM, Othman Belbeisi, a lokacin da yake magana daga Port Sudan a wani taron manema labarai a Geneva.
Ya ce kashi 71 cikin ɗari na masu dawowa sun koma jihar Al-Jazira, yayin da kashi takwas suka koma Khartoum. Sauran masu dawowa galibi suna komawa jihar Sennar.
Al-Jazira da Sennar duka suna a kudu maso gabashin babban birnin ƙasar ne.
"Muna tsammanin mutane miliyan 2.1 za su koma Khartoum kafin ƙarshen wannan shekara, amma wannan zai dogara da abubuwa da dama, musamman yanayin tsaro da ikon dawo da ayyuka," in ji Belbeisi.
Sakamkon RSF tana riƙe da kusan duk yankin Darfur na yamma, Kordofan a kudu ya zama babban filin yaƙi a makonnin baya-bayan nan.
Ya ce "yaƙin basasa mai tsanani da ban tsoro yana ci gaba da kashe rayuka ba tare da hukunci ba," yana roƙon ɓangarorin da ke yaƙi su ajiye makamai.
"Yaƙin ya haifar da bala’i ga miliyoyin mutane," kamar yadda ya ce.
"Sudan tana cikin mafarki mai ban tsoro. Dole ne tashin hankali ya tsaya," kamar yadda ya ƙara da cewa.
Comments
No comments Yet
Comment