Sport
Dollar
40,5860
-0.48 %Euro
47,7946
-0.42 %Gram Gold
4.353,4200
-1.37 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Dokar hana amfani da baburan wadda za ta rinƙa aiki daga tsakar dare zuwa wayewar gari ta shafi yankin Bakel na Senegal, wanda ke da tsayin kilomita 230 a kan iyaka da Mali.
Hukumomin Senegal sun saka dokar hana zirga-zirgar babura da daddare a wani yanki na gabashin ƙasar, bayan da 'yan ta'adda suka yi amfani da baburan wajen kai hare-hare a wasu garuruwa da ke iyaka da Mali.
Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne “saboda dalilai na tsaro,” bayan da maharan suka kai farmaki kan sansanonin sojoji a wasu garuruwan Mali a ranar 1 ga Yuli, inda aka kashe aƙalla farar hula guda.
Ɗaya daga cikin garuruwan Mali da aka kai wa hari, Diboli, na da tazarar ƙasa da mita 500 ne kacal da Kidira a Senegal.
Dokar hana amfani da baburan wadda za ta rinƙa aiki daga tsakar dare zuwa wayewar gari ta shafi yankin Bakel na Senegal, wanda ke da tsayin kilomita 230 a kan iyaka da Mali.
Kungiyar 'yan ta'adda ta JNIM, mai alaka da Al-Qaeda, wadda ke aiki a Mali, Nijar da Burkina Faso, ce ta ɗauki alhakin hare-haren da suka faru a ranar 1 ga Yuli.
Da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tuntubi gwamnatin yankin Bakel a ranar Asabar, sun ƙi yin tsokaci kan dokar da aka kafa.
Mali na fama da rikicin tsaro da tashin hankali daga ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Al-Qaeda da Daesh fiye da shekara goma.
Comments
No comments Yet
Comment