Sport
Dollar
40,5860
-0.48 %Euro
47,7946
-0.42 %Gram Gold
4.353,4200
-1.37 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan fashin sun kai hari gidan rediyon da ke Jimgbe inda suka sace kayan aikin watsa shirye-shirye da darajarsu ta kai miliyoyin naira, lamarin da ya durƙusar da ayyukan gidan rediyon na watsa shirye-shirye.
Gidan rediyon Prime FM 101.5 da ke Jihar Kogi, wanda ke ƙaƙashin Gidan Rediyon Nijeriya ya daina watsa shirye-shirye sakamakon harin da ɓarayi suka kai masa a safiyar Asabar inda suka sace kayayyakin aiki.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan fashin sun kai hari gidan rediyon da ke Jimgbe inda suka sace kayan aikin watsa shirye-shirye da darajarsu ta kai miliyoyin naira, lamarin da ya durƙusar da ayyukan gidan rediyon na watsa shirye-shirye.
Shaidu sun ce fiye da mutum 10 ɗauke da makamai ne suka mamaye gidan rediyon na tsawon fiye da sa’o’i uku kafin su arce da muhimman kayan aiki, kamar yadda jaridar Premium Times a Nijeriya ta ruwaito.
Manajan gidan rediyon, Momoh-Jimoh Adeiza, ya bayyana lamarin a matsayin “mummunan hari.”
A hirarsa da manema labarai, ya ce ma’aikatan sun gano ɓarnar da kuma satar da aka yi ne da safiyar Asabar.
“Yanzu haka ba mu watsa shirye-shirye saboda kayan aikinmu duk an sace su da karfi da yaji,” in ji Adeiza.
Ya bayyana cewa ‘yan fashin sun ɗaure ɗan sandan ɗaya tilo da ke bakin aiki a lokacin.
Mr. Adeiza ya roƙi hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ganowa da kuma kama masu laifin. Haka kuma ya roƙi taimakon gaggawa don dawo da watsa shirye-shiryen gidan rediyon.
Daniel Haruna, jami’in tsaron da ke bakin aiki a lokacin harin, ya ce maharan sun zo da bindigogi da adduna da misalin ƙarfe 1 na dare.
“Da suka haska fitila kaina, sai suka cafke ni, suka ɗaure ni da wata itaciya, sannan suka rufe min ido,” in ji Haruna.
Daga cikin muhimman kayan da aka sace sun haɗa manyan wayoyi lantarki da batiran janareto da wasu kayayyakin lantarki.
Comments
No comments Yet
Comment