Sport
Dollar
40,5860
-0.48 %Euro
47,7946
-0.42 %Gram Gold
4.353,4200
-1.37 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC ce ta gurfanar da su a kotun, inda aka tuhumi Hamisu Sa'id Yusuf, Breaker da Abubakar Ibrahim G Fresh da yin liƙin kuɗi a lokacin wasu bukukuwa.
Mai Shari’a S.M Shuaibu na Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kano a arewacin Nijeriya ta ɗaure shahararren mawaƙin Hausa Hamisu Breaker da kuma fitaccen ɗan TikTok, G Fresh a gidan yari saboda kama su da laifin wulaƙanta naira.
Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC ce ta gurfanar da su a kotun, inda aka tuhumi Hamisu Sa'id Yusuf (Breaker) da Abubakar Ibrahim (G Fresh) da yin liƙin kuɗi a lokacin wasu bukukuwa.
A sanarwar da EFCC ta fitar a shafinta na Facebook ranar Juma’a, ta ce kotun ta kama G Fresh da laifin "liƙawa da kuma tattaka takardun kuɗi ‘yan N1,000 da suka kai N14,000" a shagon wata ‘yar TikTok ɗin mai suna Rahama Saidu a watan Nuwamban 2024.
Kazalika, EFCC ta ce kotun ta kama Breaker da laifin "wulaƙanta takardun kuɗi na N200 da suka kai N30,000" yayin wani biki a garin Hadeja na jihar Jigawa a watan Nuwamban 2024.
Sai dai duka mutanen biyu sun ƙi amsa laifukansu bayan da aka karanta musu
Amma a ƙarshe shari’a ta tabbatar musu da laifin inda alkalin ya ce ya saɓa wa sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya CBN ta 2007, kuma ya yanke wa kowannensu ɗaurin wata biyar a gidan yari ko kuma tarar naira 200,000.
Comments
No comments Yet
Comment