Sport
Dollar
40,3894
-0.01 %Euro
47,2634
0.45 %Gram Gold
4.408,3700
1.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Matsalar tsadar takin zamanin tana zuwa ne duk da ikirarin da gwamnatin tarayya ta yi cewa tana raba wa manoma taki kyauta don hakan ya taimaka wajen wadatuwar abinci a kasar.
Tsadar farashin takin zamani a Nijeriya ta fara sanya manoma da dama a kasar karkata akalarsu daga noman masara da shinkafa zuwa noman gero da wake da dawa da rogo, wato tsirran da ba sa bukatar taki sosai.
Matsalar tsadar takin zamanin tana zuwa ne duk da ikirarin da gwamnatin tarayya ta yi cewa tana raba wa manoma taki kyauta don hakan ya taimaka wajen wadatuwar abinci a kasar.
Duk shekara Nijeriya na bukatar miliyoyin tan din masara da shinkafa da sauran muhimman kayan abinci, sai dai saboda yadda ake ci gaba da samun manoman suna daina noman masara da shinkafa a bana saboda tsadar takin zamani, to akwai yiwuwar za a samu ƙarancin masara da shinkafa a kasuwa wanda hakan kuma zai jawo tsadar farashinsu.
Galibin kananan manoman da muka yi magana da su sun ce ba sa iya sayen taki saboda yadda farashinsa ya yi sama sosai.
Ko da yake ya danganta da kasuwa amma yanzu ana sayar da takin Urea ne tsakanin naira 47,000 zuwa 50,000 sabanin yadda ake sayar da shi a baya a kan naira 35,000 zuwa 37,000.
Kazalika a yanzu ana sayar da takin NPK kan naira 48,000 zuwa 55,000 a yankunan karkara a Nijeriya.
Galibi manoman suna kokawa kan cewa ba zai yiwu su fita ba, idan suka noma masara wadda kudin buhunta daya ba shi da wani bambanci da kudin buhun taki.
Wani manomi kuma mai sharhi kan harkokin noma a Nijeriya Malam Bala Danja ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa hauhawar farashin kayyaki yana cikin dalilai da suka saka takin ya yi tsada.
Sannan ya ce gwamnati tana kawo takin da ta yi wa rangwamen farashi ne a makare saboda haka lokacin da aka kawo shi manoman sun riga sun sayi takin ne a lokacin da suke bukatarsa daga kasuwa.
Malam Bala ya ce wata kuma matsala da tsadar takin ta jawo ita ce yawaitar jabun takin zamani da wasu miyagu suke yi kuma hakan ke zamar wa manoma babbar matsala.
Nafi’u Muhammad Kubau wanda shi ma manomi ne, ya ce shi kansa tsarin rabon takin da gwamnati take rabawa yana da matsala saboda yawanci takin da gwamnati take bayarwa ba ya kai wa ga ainihin manoma.
Su kuma sai su sayar wa ainihin manoma da tsada.
Kazalika ya ce duk da cewa muna da kamfanonin da suke yin taki a cikin gida amma kuma ya ce galibin abubuwan da ake yin takin da su daga kasashen ƙetare ake shigo da su, saboda haka idan aka sayo kayayyakin da tsada, to hakan zai shafi farashin takin.
Sannan ya ce sai manomi ya ƙuƙuta ya rufe ido ya yi noman, sai kawai ka ga gwamnati ta shigo da abin da ya noma daga ƙetare wanda hakan ke karya farashin abin da aka noma a gida.
Kubau ya ce har sai an magance wadannan matsaloli ne za a iya samun wadatuwar abinci a Nijeriya.
Comments
No comments Yet
Comment