Sport
Dollar
40,5860
-0.48 %Euro
47,7946
-0.42 %Gram Gold
4.353,4200
-1.37 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%“Ina ganin gwamnatin Sharaa ta yi kokari wajen cika burin yankin da na al’ummar duniya duk da karancin albarkatu,” in ji Fidan a ranar Juma’a.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan ya bayyana a wata hira da kafar watsa labarai ta cikin gida cewa Isra'ila tana cin gajiyar rabuwar kai a Siriya kuma tana son ci gaba da wannan yanayin na rashin kwanciyar hankali.
“Ina ganin gwamnatin Sharaa ta yi kokari wajen cika burin yankin da na al’ummar duniya duk da karancin albarkatu,” in ji Fidan a ranar Juma’a.
Da yake tsokaci kan rawar da Amurka ke takawa a Siriya da yankin, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya ce, ban da dangantakar da Washington ke da ita da Isra’ila, Amurka ta taka muhimmiyar rawa wajen gina yankin.
Game da hadin gwiwar tsaro da Siriya, ya ce Turkiyya ko yaushe tana goyon bayan sahihin hadin kai a wannan fanni.
A farkon wannan mako, Fidan ya ce, idan kungiyoyin da ke Siriya suka yi nufin rarrabuwar kai da rashin kwanciyar hankali, Turkiyya za ta dauki hakan a matsayin barazana kai-tsaye ga tsaron kasarta kuma za ta dauki mataki.
Fidan ya ce Ankara tana son tattaunawa da kuma amsa kowace irin bukata daga kungiyoyin muddin ba ta shafi rarrabuwar kai ba.
“Isra’ila tana bin wata manufa da ke nufin raunana yankinta da kuma tabbatar da cewa yana cikin rikici,” in ji shi, yana mai cewa Isra’ila, wadda ba ta son ganin wata kasa mai zaman lafiya a yankinta, tana nufin raba Siriya.
Ya ce Ankara tana sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a kudancin Siriya, wanda ya barke bayan Isra’ila ta tsoma baki.
Yayin da daukacin al’ummar duniya da masu ruwa da tsaki a yankin ke aiki don tabbatar da cewa Siriya ba ta zama mafaka ga ta’addanci ko tushen hijira ba bisa ka’ida ba, Isra’ila tana kokarin lalata duk wani yunkuri da ake yi na tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tsaro a kasar, in ji Fidan.
Da yake jaddada cewa Turkiyya ta dade tana yin kokari sosai don kawo karshen rikice-rikice da yaki a yankin, ya sake tabbatar da kudurin kasar na ci gaba da daukar matakan diflomasiyya.
Comments
No comments Yet
Comment