Dollar

40,5860

-0.48 %

Euro

47,7946

-0.42 %

Gram Gold

4.353,4200

-1.37 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Hakan Fidan da Abbas Araghchi sun yi magana ta wayar tarho inda suka tattauna kan shirye-shiryen tattaunawar ranar Juma’a da kuma halin da ake ciki a Gaza da Syria.

Manyan jami’an Turkiyya da Iran sun yi magana game da tattaunawar nukiliya da za a yi a Istanbul

Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan da takwaransa na Iran, Abbas Araghchi, sun yi magana ta wayar tarho game da tattaunawar nukiliyar da za a yi a Istanbul ranar Juma’a.

Yayin tattaunawar wayar ta ranar Litinin, sun yi nazari kan yanayin rashin jinƙai da ake ciki a Gaza da kuma ababuwan da ke faruwa  a Syria, in ji majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya.

Za a yi wani sabon zagaye na tattauanawa kan nukiliya tsakanin Iran da ƙasashen Turai uku da aka fi sani da E3, Birtaniya da Faransa da Jamus, a birnin Istanbul na Turkiyya, ranar Juma’a.

Tun da farko, mahukuntan Tehran sun ce za su karɓi baƙuncin jami’an Rasha da China ranar Talata domin tattauna shirinsu na nukiliya.

“Muna neman shawarar waɗannan ƙasashen biyu a ko da yaushe domin hana ƙaƙaba takunkumi ko kuma rage raɗaɗinsa,” kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Esmaeil Baghaei ya shaida wa manema labarai a Tehran.

Yiwuwar ƙaƙaba takunkumin a ƙarƙshin yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015 ya bai wa ƙasashen da suka rabbata hannu a kanta damar iya sake ƙaƙaba takunkumin Majalisar Ɗinkin Duniya a kan Iran idan aka same ta da laifin rashin mutunta yarjejeniyar.

"Ba mu da shirin tattaunawa da Amurka a yanayin da ake a yanzu,” in ji Baghaei. An kasance ana tattaunawa tsakanin Tehran da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani na ƙasar Oman har zuwa lokacin da Isr’aila ta kai harin ba-zata kan Iran ranar 13 ga watan Yuni, lamarin da ya haddasa yaƙin kwanani 12.

Harin ya zo ne kwanaki biyu kafin a yi zagaye na shida na tattaunawa a Muscat, babban birnin ƙasar Oman.

Iran ta zargi Amurka da hannu a harin Isra’ila, da ya kashe manyan jami’an sojinta da masana kimiyar nukiliya da kuma fararen-hula. Amurka ta kuma ƙaddamar da hare-hare kan manyan tashoshin nukiliyar Iran uku, inda ta yi iƙirarin cewa ta lalata su. Yarjejeniyar tsagaita wuta dai ta soma aiki ranar 24 ga watan Yuni.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#