Sport
Dollar
40,5940
0.02 %Euro
46,6041
0.54 %Gram Gold
4.299,5600
0.6 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A wajen babban taron na tsaro, Turkiyya ta yi gagaɗi kan sababbin rikce-rikicen da ke addabar Gabas ta Tsakiya saboda abubuwan da Isra’ila ke yi, ta kuma zayyana matakai don cim ma zaman lafiya mai dogon zango a yankin da haɗin kan ƙasa.
Majalisar Tsaron Ƙasa ta Turkiyya ya yi kira ga ƙasashen duniya da su dauki matakan gaggawa kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa a yankin, inda ta yi gargaɗin cewa matakin da take ɗauka zai iya jefa Gabas ta Tsakiya cikin bala'i.
A cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron da shugaba Recep Tayyip Erdogan ya jagoranta a ranar Laraba, majalisar ta ce hare-haren da Isra'ila ke kai wa - da suka kama daga Gaza zuwa Iran da Lebanon da Siriya, da Yemen - sun kasance keta dokokin ƙasa da ƙasa ne da kuma tada zaune tsaye da gangan.
"Gwamnatin Isra'ila na neman jefa yankin cikin bala'i ta hanyar kisan Ƙare dangi a Gaza da kai wa Iran hari bayan shekaru da dama na wuce gona da iri a Falasdinu da Lebanon da Siriya da kuma Yemen," a cewar sanarwar.
Ta bukaci al’ummar duniya da su “sauke nauyi” kuma su yi gaggawar dakatar da ayyukan Isra’ila.
Ci gaba da tallafawa Siriya
Majalisar ta kuma yi nazari kan abubuwan da ke faruwa a Siriya, inda ta jaddada goyon bayan Turkiyya ga ƙoƙarin maido da hadin kai da zaman lafiyar kasar. Ta yi gargadi kan duk wani sabon tashin hankali ko wani yunkuri na waje na lalata ikon Syria.
Sanarwar ta ƙara da cewa, "Dole ne a daƙile hare-haren da ake kai wa 'yan gudun hijirar Siriya, da kuma duk wani mataki na 'yan aware, da ɓarna da kuma raba kan jama'a da ka iya mayar da ƙasar cikin ruɗani."
Kawar da ta'addanci daga Turkiyya
Da ta koma kan tsaron cikin gida, Majalisar ta yi nazari kan ci gaban da aka samu wajen cim ma burin gwamnati na "Turkiye da babu ta'addanci," tare da nuna cewa, nasarar da aka samu kan kungiyoyin 'yan ta'adda ta taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma shimfiɗa hanyar samun ci gaba mai ɗorewa ga manufofin ƙasa.
Sanarwar ta ce "Tare da kawar da sarƙoƙin ta'addanci, haɗin kan kasarmu zai ƙara zurfafa, kuma matakai kan manufofinmu na ƙasa za su ƙara ƙaimi cikin kwanciyar hankali da azama."
Majalisar ta kuma bayyana damuwarta kan yadda ake samun alamun ƙaruwar rincaɓewar al’amura a yakin Rasha da Ukraine tare da jaddada aniyar Turkiyya na bayar da gudunmuwar zaman lafiya mai dorewa.
Comments
No comments Yet
Comment