Tura sojojin na nuni da sabuwar alaƙar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka
Jiragen rundunar sojin Amurka guda uku masu ɗauke da sojoji da makamai sun isa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a Nijeriya, abin da ke nuna sabuwar alaƙar soji da tsaro da za ta mayar da hankali kan tallafi na tsaro, in ji jami’ai.
TRT Hausa
Jami’ai a Hedikwatar Tsaron Nijeriya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa kimanin sojojin Amurka 100 sun isa Nijeriya tsakanin Alhamis da Lahadi a matsayin rukunin farko, tare da ƙarin jirage da ake sa ran za su iso a makonni masu zuwa.
TRT Hausa
Wani jami’in tsaro ya ce sojojin Amurka za su mayar da hankali ne kan ayyukan da ba na yaƙi ba, inda za su yi aiki daga cibiyoyin bayar da umarni domin tallafa wa ƙoƙarin tsaro na Nijeriya, ba tare da shiga faɗa kai tsaye ba.
TRT Hausa
Tun da farko, kakakin Hedikwatar Tsaron Nijeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya bayyana cewa sojojin Amurka ba za su yi aikin yaƙi kai tsaye ba, illa dai bayar da goyon bayan fasaha da horo.
TRT Hausa
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun matsin lamba daga shugaban Donald Trump, wanda ya soki yadda Nijeriya ke tafiyar da martani ga hare-haren da ake kai wa wasu al’ummomi.
TRT Hausa
Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da wannan zargi, tana mai cewa rikicin tsaro na shafar Musulmai da Kiristoci baki ɗaya, yayin da take ƙara ɗaukar matakan tsaro ciki har da tura dakaru na musamman zuwa jihohin Filato da Taraba.
TRT Hausa
Hukumomin Amurka sun nuna cewa tura sojojin na wucin-gadi ne, duk da cewa ba a fayyace tsawon lokacin zamansu a Nijeriya ba.
TRT Hausa
Labarai masu alaƙa
Dakarun Nijeriya sun ce sun kashe ‘yanta’adda 42 a arewa maso gabashin ƙasar
3 kwana da suka wuce
Nijeriya ta amince da biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya naira 70,000 kudin sufuri duk wata
28 Oktoba
Mutane daga kasashe 120 na duniya ciki har da na Afirka 54 sun sayin hannayen jari a Matatar Dangote
28 OktobaGhana ta fara tattaunawa da Rasha don gina tashar makamashin nukiliya ta farko a ƙasar
Shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahama ya bayyana cewa Ghana ta fara tattaunawa da kamfanin makamashin nukiliya na gwamnatin Rasha, Rosatom, kan tsare-tsaren gina tashar makamashin nukiliya ta farko a ƙasar.
Jay-Z zai tura karamin yaron nan dan-baiwa a kwallo, Nevada Pierre zuwa makarantar kwallo a Sifaniya
Kamfanin wasanni na mawaƙin Amurka, Jay-Z, wato Roc Nation Sports yana shirin tura ƙaramin yaron nan, Nevada Pierre zuwa Sifaniya a Disamba don samun horon ƙwallon ƙasa, cewar rahotanni.
Akalla 'yan Uganda 27 sun halaka ko an yanke hukuncin sun halaka a yakin Rasha da Ukraine
Ƙasashen Afirka bakwai sun nuna damuwa kan yadda ake ɗaukar 'ya'yansu don shiga yaƙin Rasha da Ukraine.
Yawancin Karatu
