Dollar

38,7972

0.03 %

Euro

43,4144

0.84 %

Gram Gold

4.053,0700

0.44 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

“Idan Afirka ta haɗa kai bisa manufa ɗaya, za ta iya rinjayar ƙalubalen basussukanta tare da samar da ci-gaba ga jikokinmu na Afirka da za su zo nan gaba,” in ji Shugaba John Mahama.

Shugaban Ghana nemi kasashen Afirka su tsayar da manufa daya gabanin taron G20

Shugaban Ghana John Mahama ya nemi ƙasashen Afirka su tsayar da manufa ɗaya gabanin taron Ƙasashe Ashirin Mafiya Ƙarfin Tattalin Arziki a Duniya, G20 da za a yi a wannan shekara, domin neman sake tsarin basussuka mai adalci da gaskiya a kan lokaci.

Ƙungiyar G20 wadda ta ƙunshi ƙasashe 19 masu ƙarfin tattalin arziƙi da kuma ƙungiyar tarayyar Turai, ƙungiya ce da aka samar domin tattauna matsalolin tattalin arziƙi da kuɗi na duniya.

Kuma taron ƙungiyar na wannan shekarar za a yi shi ne a ƙasar Afirka ta Kudu daga ranar 22 zuwa 23 na watan Nuwamban shekarar 2025.

Kamfanin dillancin labaran Ghana ya ruwaito cewa Shugaba Mahama ya yi wannan kiran ne a taron Tarayyar Afirka da ake yi a kan basussuka a birnin Lome na ƙasar Togo.

Kamfanin ya ambato Shugaba Mahama yana cewa ya kamata ƙasashen Afirka su bar taron “da sabuwar fahimta game da bashi, inda bashi ba tamkar rikici ba ne, amma [yana tare] da ƙarfi, inda tattalin arziƙin ƙasashenmu ba za su ginu kan haƙar ma’adinai ko tallafi ba, sai dai ƙirƙire-ƙirƙire da ƙara darajar abubuwa da adalci.”

Shugaban na Ghana ya ƙara da cewa ya kamata Afirka ta sauya daga wadda ke so a sassauta mata yawan bashi zuwa wata abokiyar hulɗa dake neman sauyi.    

“Idan Afirka ta haɗa kai bisa manufa ɗaya, za ta iya rinjayar ƙalubalen basussukanta tare da samar da ci-gaba ga jikokinmu na Afirka da za a samar nan gaba,” in ji shugaban

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#