Dollar

38,7786

0.39 %

Euro

43,8944

0.27 %

Gram Gold

4.147,5900

1.06 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Sabbin hare-haren sun sanya tsoron samun karancin man fetur da tabarbarewar rikicin jinkai.

Yakin Sudan: Jiragen yaki marasa matuka sun yi luguden wuta a Port Sudan

Hare-Haren jirage marasa matuka sun faɗa Port Sudan a rana ta shida a ranar Juma’a, in ji wata majiya ta soji, inda suka ɗora laifin kan mayakan RSF da ke yaki da sojojin kasar tun watan Afrilun 2023.

“Garkuwar makamai masu linzami da muke da shi sun tare wasu jiragen yaki marasa matuka da suka kai hari birnin,” in ji majiyar, wanda ya yi magana da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Shaidu sun ruwaito cewa an kai hare-hare ta sama a Port Sudan, mazaunar sojojin da gwamnati ke marawa baya kuma cibiyar rarraba kayan taimako a kasar.

Garin mai tashar jiragen ruwa, wanda ya zama mafaka daga mummunan rikici tsakanin sojoji da mayakan RSF, na fuskantar hare-hare da jirage marasa matuka tun ranar Lahadi. RSF ba ta ce komai ba game da rikicin na baya bayan nan.

Rikicin jin kai ya rincabe

Manyan hare-hare daga nesa sun lalata wurare da dama masu muhimmanci, ciki har da filin jiragen sama na kasa da kasa guda daya da ya rage a kasar, ma’ajiyar man fetur mafi girma da babbar tashar lantari ta garin.

Garin Port Sudan ne mashigar kayan agaji zuwa Sudan, kuma Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi gargadin cewa hare-haren “na yin barazanar kara yawan bukatar jin kai da tabarbara ayyukan jin kai a kasar, in ji kakakinsa.

Yakin na fiye da shekaru biyu ya yi ajalin dubunnan mutane tare da raba fiye da mutum miliyan 13 da matsugunansu. Majalisar DInkin Duniya ta bayyana rikicin a matsayin mafi muni a tarihin rikicin jin kai.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#